Shugaban hukumar yaki da safafar miyagun kwayoyina kasa (NDLEA), Buba Marwa, ya nuna damuwarsa a kan yadda har yanzu ake kara samun masu shan kayan maye a kasar nan.
Ya ce, shan kayan maye ya kai kashi 14.4 a cikin dari wanda hakan ya kai kusan sau uku a fadin duniya.
- An Kashe ‘Yan Bindiga A Kasuwa A Zamafara
- Kwastam Ta Kama Kayan Fasa Kwauri Da Kudinsu Ya Kai Miliyan 78.6 A Kebbi
Marwa ya sanar da hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida jim kadan bayan ya kare kasafin kudin da aka kebe wa hukumarsa a cikin kasafin kudin 2023 a majalisar wakilai.
Ya ce, “Muna da kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 15 da ke shan miyagun kwayoyi, wanda wannan adadin ya kai yawan Lesotho, Swaziland, Botswana, Gambia Liberia.
“Hukumar na bai wa kwamitin tabbacin cewa, a shirye take wajen magance kalubalen shan miyagun kwayoyin da dakile noman tabar wiwi, sarrafa da safafar miyagun kwayoyin da sayar da su.
Marwa ya yaba wa kokarin da kwamitin da ke yakar shan miyagun koyoyi na majalisar ke ci gaba da yi na yakar shan miyagun kwayoyi a fadin kasar nan
Shugaban na NDLEA ya sanar da cewa, akwai bukatar a bai wa hukumar kudade da dama domin ta kara himma wajen yakar shan miyagun kwayoyi a kasar nan, musamman yadda jami’an hukumar za su dinga gudanar da aikinsu, ba tare da manyan masu hada-hadar miyagun kwayoyin sun hada yin su da kudi ba.
A kan kasafin kudin na 2022, Marwa ya bayyana cewa, an kebe wa hukumarsa Naira biliyan 38.9, wanda daga ciki Naira biliyan 10.49 na ayyukan yau da kullum za a yi da su sai kuma Naira 998.9 da kuma Naira biliyan 27.44 na manyan ayyuka.
Ya yi kira ga al’ummar da ke a yankin kudu maso gabas da su fallasa wadanda ke saffara kayan maye na Mkpuru Mmiri da wasu samari a yankin ke yin amfani da ita, an dai faro maganar wannan kayan mayen ne a shekarar 2021 a yankin.
Marwa ya ce, jami’an hukumarsa, za su ci gaba da bankado masu sarrafa ta da kuma sayar da ita.