Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa idan har aka zabe su a 2023, cikin watannin 6 kacal Asiwaju Bola Tinubu zai fatattaki ‘yan kungiyan Boko Haram.
Ya bayyana hakan ne a lokacin wata tattaunawa da ta gabata a tsakanin Tinubu da ‘yan kasuwan Jihar Legas.
- Ziyarar Da Shugabar Tanzaniya Za Ta Kawo Sin Za Ta Bunkasa Alaka Tsakanin Kasashen Biyu Zuwa Wani Sabon Matsayi
- Kumbon Dakin Gwaji Na Mengtian Ya Hade Da Tashar Binciken Sararin Samaniya Ta Kasar Sin
“A cikin watanni 6 kacal na farkon mulkin Tinubu zai kawo karshen masu tayar da kayan baya,” in ji shi.
Dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana cewa idan aka zabe shi a matsayin shugaban Nijeriya a 2023, gwamnatinsa za ta kara yawan jami’an tsaro. Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yaki da rashin tsaro a kasar nan.
A shekarar 2021, Tinubu ya yi kira da a kara yawan jami’an tsaro har guda miliyan 50, ya bayyana hakan ne lokacin da yake cika shakara 69 da haihuwa.
Sai dai kuma mai magana da yawunsa, Tunde Rahman ya bayyana cewa maganar da ya fadi tuntuban harshe ne, inda ya ce tsohon Jihar Legas yana nufin a kara daukan matasa guda 50,000 a cikin jami’an tsaron Nijeriya.