Shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Neja, Alhaji Shehu Galadima ya bayyana cewa rashin daukar tsauraran matakai kan ‘yan bindiga na iya durkusar da bangaren noma.
Shugaban kungiyar manoma ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan halin da manoman jihar ke ciki daidai lokacin da ake sa ran za a fara girbin amfanin gona.
- Alkawurana Ga ‘Yan Nijeriya Kan Tsaro, Zaman Kashe Wando Da Tattalin Arziki — Kwankwaso
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Samar Da Fa’ida A Zahiri Ga Jama’ar Afirka
Galadima ya ce yanzu haka a karamar hukumar Rafi an yi garkuwa da kananan yara su ashirin masu karancin shekaru, mata sha tara da namiji daya a garin Kusharki lokacin da suka tafi daji tsigar gyada. Ya ce washegari kuma sun yi awon gaba da wasu yaran a garin Pandogari, idan ka duba kananan manoma na tsaka mai wuya a lokacin shuka ba su tsira kuma yanzu da za a fara girbin amfanin gona matsalar na neman dawowa.
Shugaban ya ce jama’a su ci gaba da addu’a domin babu matsalar da tafi karfin Allah ya kawo karshenta, amma akwai bukatar gwamnati ta kara kaimi kar ya zama kudaden da ake warewa domin yin wannan aikin ya koma aljihun bata-gari.
Ya ce zuwa yanzu kananan manoma da dama sun fara tunanin barin noman saboda tsoro da fargabar da suke da shi na rashin ba su kariya daga hannun ‘yan bindiga wanda wannan matsalar za ta kara yawaitan rashin aiki ga jama’a da karancin abinci a cikin al’umma.
Kungiyar ta shawarci gwamnatoci da su dawo da shirin ajiyar abinci daga matakan gundumomi zuwa kananan hukumomi har jiha da tarayya domin magance fuskantar matsalolin rashin abinci.