• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ku Nisanci Shiga Siyasa, Gargaɗin INEC Ga Sabbin Kwamishinoninta

by Sulaiman
3 years ago
INEC

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya gargaɗi sababbin kwamishinonin zaɓe cewa su nisanci shiga harkokin siyasa ko yin tarayya da ‘yan siyasa, sai fa a bisa ƙa’idar da doka ta tanadar.

Yakubu ya bukace su da tabbatar su na bin dukkan tsare-tsaren da dokar zaɓe ko dokar ƙasa ta shimfiɗa wajen gudanar da aikin su.

  • 2023: INEC Ta Samar Da Ingatattun Tsarukan Gudanar Da Tsaftataccen Zabe

Shugaban ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da ya ke rantsar da sababbin Kwamishinonin Zaɓe 19.

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Ya ce ya zama tilas su kasance su na aiwatar da komai a bisa ƙa’ida, ba tare da nuƙu-nuƙu ko fifita wani ɓangare ba.

Yakubu ya ce: “Kuma a duk lokacin da ku ke ganawa da masu ruwa da tsaki, to ku kasance ba ku wuce ƙa’idar da dokar ƙasa ta gindaya maku.

INEC
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya na musabiha da sababbin kwamishinonin zaɓen da aka rantsar

“Haka ma a yayin tuntuɓar juna tsakanin ku da jama’a, kada ku tsallake iyakokin da dokar ƙasa ta hana ku tsallakawa.

“Sannan ku nisanci kai ziyara ofishin gwamna. Wato ba a son a gan ku gidan gwamnati. Kuma kada su riƙa keɓewa ku na ganawa da ‘yan siyasa ba bisa ƙa’idar aikin ofis ba. Ko bayan tashi daga ofis, ba a yarda su riƙa keɓancewa da ‘yan siyasa ba.

“Ku tuna gwamnatin tarayya ku ke wa aiki, saboda haka ita ce abin biyayya a gare ku. Don haka kada ku kauce daga turba, gudun kada ku kai ga zubar da ƙimar ku da darajar INEC.

“Kuma ina ƙara jaddada maku cewa hanyar amfani da tsarin tantance sahihiyar rajistar zaɓe ta BVAS ce kaɗai hanyar da aka amince a tantance mai rajistar zaɓe.”

Daga cikin sababbin kwamishinonin da Yakubu ya rantsar akwai Uzochukwu Chijoke a Jihar Abiya, Nuru Inusa a Adamawa, Elizabeth Agu a Anambara, Mahmood Nura a Bauchi, Samuel Egu a Binuwai, Yomere Otitsemolebi a Kuros Riba da Onyeka Ugochi a Ebonyi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
Manyan Labarai

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba
Manyan Labarai

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Next Post
Shin Ko Liverpool Za Ta Iya Kai Bantenta A Bana Kuwa?

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025
Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.