A jiya ne, aka bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na biyar (CIIE) a birnin Shanghai.
A jawabin da ta gabatar ta kafar bidiyo yayin bude bikin baje kolin, babbar darektar kungiyar cinikaya ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa, kasar Sin ta zama kasar dake kan gaba a duniya wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare, kana kasa ta biyu a fannin shigo da kayayyaki da samar da hidima a duniya.
Rawar da kasar din take takawa a harkokin cinikayyar kasa da kasa da ma tsarin kasancewar bangarori daban-daban, na da muhimmmanci matuka.
Dr Ngozi ta kuma yi nuni da cewa, yadda kasar Sin ta halarci taron ministocin kungiyar karo na 12 da irin goyon bayan da ta bayar, duk sun haifar da kyakkayawan sakamako.
Ta ce, shirya bikin baje kolin, ya nuna cewa, kasar Sin za ta iya taimakawa wajen tabbatar da cewa, harkokin cinikayya sun kasance wani karfi na samun bunkasuwa da damawa da kowa da kowa.
Don haka, tana fatan yin aiki da kasar Sin da sauran mambobin WTO, don gina tsarin kasuwanci mai karfi da inganci a duniya baki daya, da samar da gudummawa ga daukacin bil-Adama da ma duniyarmu. (Ibrahim)