• English
  • Business News
Thursday, September 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matakan Da Suka Kamata A Bi Wajen Hada Abincin Kaji Don Su Yi Saurin Girma

by Abubakar Abba
3 years ago
in Noma Da Kiwo
0
Matakan Da Suka Kamata A Bi Wajen Hada Abincin Kaji Don Su Yi Saurin Girma
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Akwai matutar muhimmanci ga mai kiwon kajin gidan gona ya san yadda zai hada abincin kajinsa da kansa musamman masu kiwon Kajin gidan gona masu saurin girma da ake kira a Turanci, da broilers.

Masara:

Za a sami masara kilo 50 sai a hada ta da abinci kilo 100 na buhu hudu ke nan ko kuma kilo 25 ga wanda zai hada buhu 2, kawai dai duk adadin da mutum zai hadd zai iya samun adadin da ya yi daidai da jadawalin wannan kiyasi wato kari daga kan kilo 50 zuwa sama ko zuwa kkasa adadin dai kawai shine a raba gida biyu ko ninkawa gida biyu misali abinci buhu biyu ana bukatar masara kilo 25 , buhu daya kuma masara kilo 12.5. amma kafin a auna adadin da za ayi amfani da ita sai a kai inji a nukata kamar yadda ake bukatata  sai a yi nikan ya yi dan laush.

Waken suya:

Anan za a sami waken suya kilo 10 ga wanda zai hada buhu hudu kilo 100, kilo 5 ga mai hada buhu 2, kilo 2.5 ga mai hada buhu 1, amma ana bukatar waken ya kasance an nika shi kar yadda aka yi bayani a masara kafin a auna ko ahada da sauran kayan hadin, kafin a nika a soya shi kadan domin kone waddansu sinadarai dake kawo rashin saurin narka abinci a cikin kaji.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe

Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025

Yanda za a soya shi kuma za a nemo yashi a zuba a cikin tukunya ko kwanon suya babba a dora akan wuta a rika juyawa bayan yashin ya danyi zafi a zuba waken suyar a ciki a rika juyawa akai akai har zuwa dan wani lokaci misalin mintuna 5 har zuwa 20 idan bai soyu ba ya dai danganta da yanayin zafin wutar da aka rura take, amma anan ina son mai wannan suya kada ya bari waken suyar ya kone da yawa don idan ya kone dayawa babu wani amfani da zai yi saboda za a kone harda masu amfanin da ake bukata don haka idan za ayi suyar a soya kamar yadda ake soya Gyada

Kwakwar Manja:

Kuli-kuli:

Ana samunsa kamar yadda yake a hoton da yake kasa.Idan abincin buhu 4 za ayi sai a yi amfani da kilo 12  ne kawai, idan kuma buhu 2 ne da kilo 6 Kwakwar za a yi amfani, haka kuma ga wanda zai yi buhu 1 sai yayi amfani da kilo 3 a hada.

Oyster shell :

Wannan ana amfani da shi ne idan dusar finisher za a hada domin yana dauke da calcium sosai wanda ke sakawa kaji kkarfin kashi wanda zai taimakawa kajin samun karfin jiki dana kafafunsu.

Ana son abincin da za hada ya kai kilo 100kilo ne wato buhu 4 kenan ana amfani da kilo  1 ne na Oyster shell, idan kuma buhu 2 ne kilo 0.5 za a saka, kilo 0.25 a buhu 1.

Bone meal ko fish meal:

Sai Bone meal ko fish meal ga wanda zai hada kilo 100, buhu 4 zai yi amfani da 3kg na Bone meal ko fish meal wato a buhu 4 kenan, idan kuma kilo 50 ne buhu 2 za’ayi amfani da kilo 1.5 0.75 ga wanda zai hada buhu 1 kilo 25.

Sandarin Bitamins da na Minerals Premid:

Wannan shi kuma za a zuba kilo 0.25 a buhu 4, kilo 0.125 a buhu 2, 0.kilo 062  a buhu 1.

Methionine:

Za a zuba kilo 0.3 a buhu 4 kilo 100 ds kilo 0.15  a buhu 2 sai kilo 50 da kilo 0.75  a buhu 1 na kilo 25.

Lysine:

Wannan shi kuma za a zuba kilo 0.25kg a buhu 4, kilo 0.125 a buhu 2, 0.sai kuma kilo 0625  a buhu 1.

Gishiri:

Wannan ana amfani dashi dan kadan, kilo 0.2 a buhu 4 kilo 100, kilo 0.1  a buhu 2, kilo 50 , kilo 0.05 a buhu 1 kilo 25 .

Gishiri yana da matukar amfani a cikin sinadaran hada abincin kaji domin idan yayi karanci matsala ce, saboda mafi yawancin abincin kaji idan kuka ga yaki saka kaji girma zai iya yiyuwa tun a kamfani aka sami matsala wajen saka gishiri saboda gishiri yana budewa kaji ciki suci abinci,yana kuma saita yanayin jikin kaji yana kuma aikin bada kariya wajen halittu masu hadari a cikin kaji. Amma yana da kyau a kula idan gishirin yayi yawa yana kawo matsaloli wanda suka hada da mace-macen kaji.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Abincin KajiBroilersKajiKiwo
ShareTweetSendShare
Previous Post

Adawar Siyasa: ‘Yan Siyasa Sun Fara Kewaya Wa Junansu Al-kur’ani A Yobe

Next Post

Karyar Lefe Dozin A Tsakanin Maza

Related

Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe

2 weeks ago
Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025
Noma Da Kiwo

Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025

2 weeks ago
Kwararre Ya Ja Hankali Kan Sayar Da Takin Zamani Da Ba A Tantace Shi Ba
Noma Da Kiwo

Kwararre Ya Ja Hankali Kan Sayar Da Takin Zamani Da Ba A Tantace Shi Ba

3 weeks ago
Manoman Doya 100 A Jihar Nasarawa Suka Amfana Da Horon Cibiyar NEPC
Noma Da Kiwo

Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu

3 weeks ago
Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai 
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai 

4 weeks ago
Abubuwan Da Suka Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Tsarin Noman Waken Soya
Noma Da Kiwo

Abubuwan Da Suka Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Tsarin Noman Waken Soya

4 weeks ago
Next Post
Karyar Lefe Dozin A Tsakanin Maza

Karyar Lefe Dozin A Tsakanin Maza

LABARAI MASU NASABA

Babban Sha’anin Dan Adam Na Wanzar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaba Zai Samu Nasara

Babban Sha’anin Dan Adam Na Wanzar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaba Zai Samu Nasara

September 4, 2025
Dakarun PLA Sun Gudanar Da Sintiri A Yankin Tekun Kudancin Sin

Dakarun PLA Sun Gudanar Da Sintiri A Yankin Tekun Kudancin Sin

September 4, 2025
Spence Na Dab Da Kafa Tarihin Zama Musulmi Na Farko Da Zai Buga Wa Ingila Ƙwallo

Spence Na Dab Da Kafa Tarihin Zama Musulmi Na Farko Da Zai Buga Wa Ingila Ƙwallo

September 4, 2025
Gwamna Sule Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Fara Yaƙin Neman Zaɓe A Nasarawa

Gwamna Sule Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Fara Yaƙin Neman Zaɓe A Nasarawa

September 4, 2025
Xi Ya Gana Da Shugaban Zimbabwe Da Na Jamhuriyar Kongo

Xi Ya Gana Da Shugaban Zimbabwe Da Na Jamhuriyar Kongo

September 4, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Kim Jong Un

Xi Jinping Ya Gana Da Kim Jong Un

September 4, 2025
Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Ba Da Gudummawarta Wajen Kiyaye Zaman Lafiya Da Ci Gaban Duniya 

Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Ba Da Gudummawarta Wajen Kiyaye Zaman Lafiya Da Ci Gaban Duniya 

September 4, 2025
Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai

Tinubu Ya Fara Hutun Aiki Na Kwanaki 10 A Faransa Da Birtaniya

September 4, 2025
Ibtila’in Ambaliyar Ruwa: Halin Da Birnin Maiduguri Ya Tsinci Kansa A Ciki

Gargaɗi: Ƙauyuka 43 A Jihohi 14 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa 

September 4, 2025
Hakimin Da Aka Sace A Jihar Kogi Ya Shaki Iskar ‘Yanci

Hakimin Da Aka Sace A Jihar Kogi Ya Shaki Iskar ‘Yanci

September 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.