A ci gaban tattaunawar da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta yi da fitacciyar Jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, kuma me taka rawa a cikin shirun Dadin Kowa wato HAJIYA SADIYA LAWAN MUSA wadda aka fi sani da SABUWAR MALAM AYUBA .
Ta bayyana gaskiyar rade-radin da wasu mutane ke yi na alakarta da Dan Asabe da kuma dan gidan Malam Barau a shirin Dadin Kowa, ta kuma bayyana wasu matsaloli da ‘yan Kannywood ke fuskanta a cikin masana’ar Kannywood, haka kuma ta yi kira ga gwamnati don magance wasu matsaloli da ke addabar cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, har ma da wasu batutuwan. Ga dai tattaunawar kamar haka:
- An Kebe Rumfunan Nune-Nune Shida A Bikin CIIE Karo Na 5
- Ambaliya: Tallafin NEDC Ya Zo A Kan Gaba A Arewa Maso Gabas
Kamar misali in aka yi wani abu na gaske, duka ko cizo ko mari ko makamancin haka, shin ana kara kudi ne fiye dana sauran da ba a yi wa ba ko kuwa duk kudi daya ne?
Toh! dai duk kudi daya ne ba a kara komai, wani zubin ma idan akai na gasken sai dai kawai ayi nishadi ayi dariya, ba a kara kudi.
A baya na ji kin ce kafin ki fara shirin Dadin kowa kin yi fina-finai sun kusa Hamsin, ko za ki iya tuna adadin fina-finanki gaba daya a yanzu?
Gaskiya ba zan iya cewa ga adadin fina-finai na gaba daya na, saboda shekarun sun Tura, kuma koyaushe dai akan aikin ake ba ji ba gani, wasu ayyuka ma ni yanzu ba ma na sanin sunansu sai dai kawai in an ce an ganni a fim kaza sai na ce me nayi a cikin fim din , toh sannan ma zan iya gane fim din da aje nufi, saboda abun yayi yawa tun kana lissafi tun kana doki, har sai ka zo ma baka iya lissafin abin da kayi.
Ko akwai wani Kalubake da kika taba fuskanta a game da harkar film?
Ni dai a cikin har kar nan ta fim ban taba samun wani kalubale na, abin da kawai guda daya da yake damuna shi ne; in ma fita aiki bana so na ga na yi dare, kuma yawamci aiki din in na tafiya wani nesa ne ko na tafiya wani gari ban cika sonshi ba, ko da an gayyace ni ma yawanci in na tafiya nesa ne bana yi, sai na hakura kawai na zauna sabida yara.
Kamar masu kallo da makota ko ‘yan uwa haka, shin ba kya samun kace na ce daga garesu game da wannan sana’a taki?
Gaskiya dai babu bangaren dana samu wannan matsalar sai ta bangaren maigidana shi ne na so na samu matsala ta bangaren ‘yan uwanshi da iyayensa, amma da suka zo shi ma kuma kanshi ya nuna musu cewar shi ya barni na yi, kuma ya kafe saboda ya san irin taimakon da nake yi a gida, namiji ko ya kawo ko bai kawo ba kai za ka yi, ka kula da ‘ya’yanka kai musu komai, kuma ba wata harka ya ga ka je kana yi da wasu mutane na banza ba, ka kama mutuncin kanka, har abokan arzikin ma da makobta, wallahi kullum yabona suke yi, suna cewa gidana kamar ba gidan ‘yar fim ba, sabida wani lokacin ana ganin kamar ‘yan fim suna da tara jama’a ko wani abu dai haka, sai a rinka cewa to wai gidana jamar ba gidan ‘yan fim ba, ba ka ganin wani shige da fuce ba ka ganin kowa. Toh kin ga sakamakon auren nan da kake da shi dole ne ka kama kanka, ka nutsu, dan wasu ma wadanda ba su san ma ina da aure ba indai suka ji daga baya suka ji labarin ai ina da aure sai su ce haba! shiyasa muke hanin tana da kamun kai, wallahi ban taba samu matsala ba sai a bangaren dangin mijina kuma su ma daga baya daya nuna musu cewa shi ya barni ba wata matsala ya nuna dari bisa dari yana goyon bayana shi ne suka hakura su ma suka kyale suka dawo kuma aka zauna lafiya da su.
Wanne irin nasarori kika samu game da harkar film?
A gaskiya dai na samu nasarori ta hanya daban-daban, saboda na samu jama’a wanda suke kaunata, suke kuma nuna mun kauna da abubuwa na alkhairi, sannan kuma a cikin harkar fim dinnan na samu nasarori sosai ta hanya daban-daban da ban taba tunanin zan samu ba, saboda wani abun ko ta bangaren ilimin yara na samu nasarori akan wanda za su tsaya su taimaka musu ko kana neman wani abu, ka samu wanda zai jajirce, zai tsaya maka ka je, abin da ko da kudinka ma ba za ka iya samunsa ba, sai ka ga wani dalilin yana ganinka a fim daya ganka zai taimaka maka. Sannan kuma ta bangaren samun alkhairai ita kanta a indostiri din ma, bangarori na ‘yan siyasa da sauransu duk ana samun taimako ta bangarensu. Kuma nasarori dana samu ina zaune ba ni da wani abu na kamawa, babu Jari a hannuna to harkar da nake yi na fim din nan a ciki nake samun abin da zan zo na ci da kaina na ci da ‘ya’yana, in yi mana sutura, tun ina gidan haya ma mu biya kudin haya duk da shi muke yi harkar fim din nan, kin ga kuwa na samu babbar nasara a harkar fim dinnan kuma ya sani na san jama’a sosai ba na a Najeriya kadai ba har da kasashe na waje, dalilin wannan harkar fim din, ina alfahari da hakan.
Za ki ji wasu na maganar cewa kudin da ake bayarwa na sallama, ba wasu kudi ne na azo a gani ba har da zai isa yin wasu abubuwa masu yawan gaske , ya za ki fahimtar da masu karatu akan wannan batun?
A gaskiya dai ita wannan harka ta mu, dole mutum sai ya nutsu ya san me yake, saboda ita wannan harkar akwai manya-manyan furodusas akwai kuma kanana. A gaskiya wasu yaran ma matasa ne kanana da za kiga da sun ta so sai su ce sai sun yi fim, sai su je su samo dan labarinsu da ‘yan kudinsu da bai taka kara ya karya ba, bai wuce kudin shan fiyo wata ba, su ce za su yi fim. To irin wannan in ka hadu da su toh gaskiya baka samun yadda kake so, amma gaskiya duk furodusan da yake cikakken furodusa ne kuma an san shi yana yin aiki ba yadda za ai kai masa aiki bai sallameka ba, ya baka abin da ya ga ya dace dai-dai karfinsa shi ma zai baka, tun da ita indostiri ba wai kudi ne aka yanke ba aka lika a jikin bango aka ce wanda yayi scene kaza za a bashi kaza ba haka bane, ya danganta da aljihun furodusa, haka kuma yanayin biyan, aikin mutum haka yake, gaskiya. Amma idan mutym yayi karo da irin wannan kanana-kananan furodusas din da sun shigo ne kawai suma ba su san kan abun ba sai su je su dan hado kudinsu, wani ma abokaine za a yi karo-karo sai a zo a hada kudi a ce mu je muma mu yi namu fim din, toh idan ka fada hannun irin wannan toh shi ne fa kake samun ba dai-dai ba, wani ma sai kai aikin ma wallahi ba su baka ko naira daya ba, ka dai ci abinci wani ma da ganganma za su rokeka ba za ma su boye maka ba za su ce Mama za ki mana aiki ne amma gaskiya wallahi ba mu da kudi na mota kawai zamu baki, da yake yawanci ana tare wani za ka je kayi mishi ma kai kanka ba ma za ka karbi kudin shi ba tun da ka san ba shi da shi, shi ma dai kokari yake ya samu ya ga cewa shi ma ya dan taso an sanshi. Toh shiyasa wallahi irin wannan dai gaskiya in mutum ya hadu da irinsu sai dau yayi hakuri, amma gaskiya duk furodusas din da ya kiraka aiki indai dama ya riga ya san abin da yake yi ba zai taba kiranka bai sallameka ba gaskiya, za a baka abinci, za a kuma kudin aikinka, wani ma za su tambayeka ma ko kai ka tambayesu me za ku bani?, za mu baka kaza toh sai ka je kayi musu aikinka in ka amince. Idan kuma kun yi da su ka ga baka amince ba kin ga ba za ma ka je ba, wasu kuma za su kiraka su fada maka daret su ce gaskiya Mama ba mu da kudi amma in za ki zo ki mana toh kudin mota za mu baki, da yawa ni na yi wa irin wadannan yara-yaran na musu tun da ana tare ana haduwa wajen ayyuka, sai ka ji yaro ya zo ya durkusa ya gaisheka Mama to ni ma nan gaba zan yi nawa aikin amma taimaka mana za a yi muma mu samu mu dan taso, toh irin wannan daman baka ma sa rai da wani abu gaskiya, amma wai ka je kai aiki haka kawai kai tsaye a dauko wani abu bai taka rawa ya karya ba ni dai ban taba haduwa da wannan ba wallah, ban taba haduwa da shi ba, saboda duk yawanci in na ga ma aiki ma wanda na san bai taba kirana aiki ba ban taba aikinsa ba sai na kira wasu na tambayesu ya wane yake kuwa, kuna ganin zai maka sallama na mutunci ko kuwa? zan samu liket kafin ma na je wajen aikin mutum.
Ya kika dauki dsana’ar film a wajenki?
Na dauke shi sana’a mai tsafta ma kamar yadda na fada miki a baya, dan ina gayawa jama’a ina cewa ban taba ganin sana’a da kake samun halak dinka a cikinsa ba irin fim. Abu ne za ka je kayi magana da bakinka da guminka, wani zubin za a yi shutin a cikin rana , haka za ka tsaya a cikin ranar nan ta kare akanka, in ya kama a tsakar gida ne, a cikin rana komai zafin rana a cikjnta za a yi, haka zalika komai sanyi a cikin sanyin za a yi, idan kuma shutin ne za a yi scene a cikin daki za a saka fitulun nan masu zafi ina da hawan jini wani zubin zafin fitulun nan yana kara tayar mun da hawan jini na, lokacin da mukai ayyuka a cikin daki falo za a zo a saka fitulu ka ji gumi, jikinka ya dauki zafi, idanunka duk su dauki ciwo, shiyasa nake fadawa mutane nake cewa ban taba ganinma sana’a ta halak tun da abu ne za ka yi shi da karfinka da guminka, da jikinka, sannan kuma kana gamawa a dauki kudinka a baka ka tafi gida, toh ni shiyasa ma harkar fim ma na dauke ta nake sha’awarta kuma har na sa ‘ya ta ma cikin fim din.
Za mu ci gaba mako mai zuwa