Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana ibtila’in ambaliyar ruwa ta bana a jihar Bayelsa a matsayin kalubale mai girma wanda ya cancanci duniya ta maida hankali a kai.
Jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya kuma wakilin babban sakataren MDD Matthias Schmale ne ya bayyana hakan a jiya a lokacin da ya jagoranci wata tawaga da ta kunshi jami’an kungiyoyin duniya da na hukumar lafiya ta duniya da ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya a ziyarar ban girma da suka kai wa Gwamna Douye Diri a Yenagoa a ranar Asabar.
Schmale ya kwatanta ibtila’in ambaliyar ta Bayelsa da wacce ta afku a Pakistan wacce ta kada hankulan duniya.
Kodinetan na Majalisar Dinkin Duniya wanda a ranar Juma’ar da ta gabata ya samu rakiyar Gwamna Diri zuwa wasu al’ummomin da ambaliyar ruwan ta shafa a karamar hukumar Ijaw ta Kudu, ya ce ziyarar tasa, ta zo ne sabida wasikar da Gwamnan ya rubuta musu, inda ya yi kira da tallafawa, don magance mummunar illar da ambaliyar tayi.
Ya kuma bayyana cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta daukaka maganar zuwa inda ta dace don kawo tallafi da maida wadanda ibtila’in ya shafa ga matsugunansu, kuma su cigaba da rayuwarsu ta yau da kullum.