Makarantun Sheikh Khalifa Ishaka Rabi’u Khadumul Kur’an guda biyu da Gwani Yusda Legend ke jagoranta, sun gudanar da bikin yaye dalibai 887 a lokaci guda, wanda aka bai wa kowani dalibi kyautar Naira 30,000 a matsayin ihsani daga iyalan Shiekh Ishaka Rabi’u.
A lokacin bikin yaye daliban makarantar khalifa Sheikh Ishaka Rabi’u da ke unguwar Sani Mai Nage ta yayi dalibai mahadata alkur’ani 800, sai kuma kwalejin Khalifa Ishaka Rabi’u da ke unguwar Goron Dutse bangaran karatun zamani wacce ta yaye dalibai guda 87 wanda ya ba da adadin dalibai 887.
- Yin Tsari Don Maganin Mantuwa A Kasuwanci
- 2023: Kotu Ta Kori ‘Yan Takarar Majalisar Wakilai 3 Na Jam’iyyar LP A Ribas
Wannan bayanin ya futo ne daga bakin, Alhaji Rabi’u Ishaka Rabi’u wanda aka fi sani da Alhaji Karami IRS a lokacin da yake jawabi a wajen taron. Ya kuma kara da cewa wannan aiki na mahaifinsu na ci gaba da samun nasara a ko da yaushe domin kowa yanzu haka sun karbi takardun shaidar izini na bude jami’ar KHAIRUN wace Khalifa Sheikh Ishaka Rabi’u ya kafa irinta ta farko ta Alkur’ani a Nijeriya mai suna Khalifa Ishaka Rabi’u Unibersity take Kano.
Ya kara da cewa wannan yinkuri na daukar dalibai da fara karatu a jami’ar KHAIRUN a farkon shekarar 2023 abu ne da ke nuna burin Khalifa na alkairi da ya cika kuma za mu kara wasu sabun tsangayu a kan wanda Khalifa da kansa ya yi.