Yara 21 da aka yi garkuwa da su a unguwar Mairuwa da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina sun shaki iskar ‘yanci.
Kakakin rundunar ‘yan sanda, SP Gambo Isah ne ya tabbatar da samun ‘yancin su a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce, wadanda aka sacen da suka hada da ‘yan mata 17 da maza 4, an hada su da iyalansu amma ana ci gaba da bincike.
Talla
“Ina mai farin cikin sanar da sakin dukkan yara 21 da aka yi garkuwa da su a lokacin da suke aikin gona a kauyen Mai Lafiya da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
“An sake su, kuma tuni aka hada su da iyalansu. Ana ci gaba da bincike kan lamarin”, in ji shi.
Talla