Gwamnatin jihar Kano ta yi Allah-wadai da kakkausar murya da ikirarin wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta Sahara Reporters da ta yi na cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na daya daga cikin gwamnoni uku da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annuti (EFCC) ta bayyana da boye kudade a gidajensu.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa, hukumar EFCC ba ta lissafa sunayen gwamnonin da take zargi ba, amma Sahara Reporters ta bayyana sunan gwamnoni akan karya.
Ya ce rahoton da kafar ta fitar, ba shi da tushe a labaran bincike, sai dai kawai hasashe na mawallafa ko kuma wani yunkuri na bata sunan gwamnan da gangan.
Malam Garba ya yi nuni da cewa, Gwamna Ganduje bai boye Biliyoyin Nairori a gida ba don biyan ma’aikatan gwamnatinsa albashi, sabida gujewar faduwar banki.
Kwamishinan ya kara da cewa jihar Kano na daya daga cikin jihohin tarayya da ke biyan albashin ma’aikata akan lokaci, a lokacin da Sahara Reporters ta fitar da rahoton karya, an fara ba wasu Ma’aikatan jihar albashin watan Oktoba.
Don haka ya yi kira ga kamfanin Sahara Reporters da ta janye labarin tare da neman gafarar gwamnatin ba tare da bata lokaci ba, gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin shari’a.