Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta amince da kudirin dokar gwamnatin jihar domin kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
A ranar Litinin ne majalisar ta zartar da kudurin dokar kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa tare da kyautata zaton cewa za ta yi tasiri mai inganci ga jami’an gwamnati da sauran daidaikun mutane a harkokin kasuwanci iri-iri.
- Shugabannin Sin Da Madagascar Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafuwar Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Su
- Zan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Gyara Tattalin Arzikin Nijeriya – Peter Obi
Majalisar ta ce ta samar da kudirin dokar yaki da cin hanci da rashawa domin taimakawa sauran hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a jihar.
‘Yan majalisar sun jaddada cewa, idan har gwamna Ahmadu Fintiri ya amince da kudurin dokar kuma ya zama doka, zai samar da gaskiya da rikon amana da kuma magance laifukan kudi baki daya.
Kudurin dokar mai taken ‘Kudirin dokar da za ta samar da kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Adamawa’, Hon. Abubakar Isa, dan majalisa mai wakiltar mazabar Shelleng.
Amincewar a ranar Litinin din ya biyo bayan nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin shari’a da ci gaban ‘yan kasuwa, wanda mataimakin kakakin majalisar, Hon. Pwamwakeno Mackondo, dan majalisa daga mazabar Numan.
Bayan zartar da kudirin dokar, shugaban majalisar Rt. Hon. Aminu Iya Abbas, ya umarci magatakardar majalisar da ya fitar da wani don bai wa gwamna Ahmadu Fintiri.