Kimanin mutum 74 ne aka kwantar a asibiti, motoci sama da 100 aka farfasa a wani farmakin da yan dabar siyasa suka kai wa tawagar dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a lokacin da ya ziyarci birnin Maiduguri ta jihar Borno a gangamin yakin neman zaben da jam’iyyar ta gudanar da yammacin ranar Laraba (yau).
Mai magana da yawun kwamitin yakin zaben Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye shine ya shaida hakan a yayin gangamin yakin zaben jam’iyyar da aka gudanar a Maiduguri, ya zargi jam’iyyar APC da kokarin dakatar da gangamin yakin zaben ta hanyar dauko hayar ‘yan daba domin su farmakesu.
Melaye ya kara da cewa jam’iyyar da ke mulki a jihar ita ce dauko hanyar ‘yan daban inda suka farmaki tawagar PDP da duwatsu, adduna, barandami sa’ilin da tawagar ta bar fadar Sarkin Borno zuwa dandamali Ramat Square domin gudanar da babbar gangamin yakin zabe na jam’iyyar PDP, dukka a cewarsa domin kawo tsauro da cikas ga taron.
Ya nuna cewa an jibge ‘yan daban a lunguna da sako-sako don farmaki magoya bayan PDP.
Sen Melaye ya kara da cewa, “Amma su sani, ina tabbatar musu babu wani da ya Isa ya dakatar da mu.”
LEADERSHIP ta labarto cewa sama da motoci 10 ne aka lalata a kusa da Bulumkutu da ke cikin Birnin jihar.
Bayan da tawagar Atiku suka wuce, an gano motocin kashe gobara suna ya kokarinsu na kashe wutar da magoya bayan APC da ake zargin da bankawa motocin.