Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta jihar Ekiti (NDLEA) ta lalata wata gonar da aka shuka tabar wiwi mai fadi a jihar Ekiti.
Gonar na cikin wani daji ne da ke Ire Ekiti a karamar hukumar Oye , inda aka shuka tabar na da nisan kilomita 20 tsakaninsa da wani kauye. Bayan gano wannan gonar ce jami’an na NDLEA suka lalata dukkan abin da ke cikin gonar.
Da yake yi wa manema labarai bayani, jim kadan bayan samun wannan nasara ta su mataimakin kwamandan hukumar ta NDLEA din, na jihar Ekiti Mista Mohammed Ibrahim, ya ce, yanzu haka sun samu nasarar kama mutum takwas wadanda ake zarginsu da sa hannu a wannan gona.
Kamar yadda Ibrahim, wahda ya jagorancin tawagar NDLEA suka shiga dajin, ya bayyana “sun kama tabar wiwin mai nauyin kilgiram 1,465, sannan juma sun kama mutum takwas da ke da alaka wannan taba.
“Mun kawo samfurin tabar wiwin da muka kama ofishinmu na NDLEA da ke Ado Ekiti.
“Yanzu haka muna ci gaba da bincike, domin gano wasu wuraren in akwai su” in ji shi.