Hukumar zaɓe a Nijeriya ta musanta rahotannin da ke yaɗa cewa tana bincike kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, Bola Ahmed Tinubu.
BBC ta rawaito cewar a ranar Juma’a ne wata sanarwa da aka alaƙanta da Independent National Electoral Commission (INEC) ta ce hukumar na gudanar da bincike kan wani lamarin kotu na 1993 inda gwamnatin Amurka ta ƙwace wasu kuɗaɗe daga hannun Tinubu.
- INEC Ta Samar Da Tsarin Yadda ‘Yan Gudun Hijira Za Su Yi Zabe A Zamfara
- Mu Masu Bin Dukkan Umurnin Kotu Ne —Shugaban INEC
Sai dai cikin wata sanarwa a ranar Asabar, INEC ta ce labarin na ƙanzon-kurege ne.
“Wata sanarwa da ta dinga waɗari a shafukan zumunta da aka ce INEC ce ta fitar ta yi iƙirarin cewa mun ƙaddamar da bincike kan wani laifi a Amurka da ya ƙunshi wani ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa don tantance ko ya karya dokokinmu na Dokar Zaɓe ta 2022,” a cewar sanarwar da Festus Okoye ya saka wa hannu.
“Muna tabbatar da cewa sanarwar ba daga wajenmu ta fito ba kuma ba ma gudanar da wani bincike. Aiki ne na masu tayar da zaune tsaye kuma [sanarwar] ta boge ce.”