ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sake Kunno Kan Siyasar Kabilanci

by Idris Aliyu Daudawa
4 years ago
Siyasar kabilanci

Sau da yawa idan jam’iyyar da ke kammala mulki a wa’adinta na biyu kuma tana cikin takarar zaben Shugaban kasa, hankalin wasu mutane ya fi tashi, ganin cewa ko za su rasa wani tagomashin da suke samu daga kasancewar ita gwamnatinidan bata kai labara ba.

Akwai fadin gaba,saboda rudar wasu ne daga cikin Talakawa wadanda ake nuna masu cewa me yiyuwa su shiga cikin halin tagaiyara in suka zabi wata jam’iyya daban,idan sabuwar gwamnati ta hau musamman ma idan ta adawa ce.

  • ‘Ya’yan Jam’iyyar PDP Sama Da 1,000 Sun Sauya Shekar Siyasa Zuwa APC A Zamfara

Ita dai gwamnati wadda take rike da kambun mulki na kasa tun wa’adinta na farko ne take fara yi ma kanta kamfe,na kodai su al’ummar kasar su yanke shawarar sake zabenta, bayan ta kammala wa’adinta na biyu.Halin da kuma ake ciki ke nan yanzu babu kuma damar a mayar da hannun agogo baya.

ADVERTISEMENT

Shugaban kasa ba shi kadai bane da zai yi dukkan ayyukan da za su amfani al’ummar kasa ba.Akwai mataimakinsa, Ministoci, Gwamnoni, ‘Sanatoci, ‘yan majalisun tarayya, na Jihohi, Shugabannin kananan hukumomi,kai har ma da Kansiloli,da sauran wadanda suke rike da mukaman siyasa, kowanne daga cikinsu yana da gudunmawar da zai bada, idan Talakawa suka gamsu kan abubuwan da suka yi, har ya burgesu, suka ji dadi za su sake zabenta.Idan kuma aka samu akasin haka to kowa fa sai ya san inda dare yayi ma shi ke nan.

Domin kuwa Hausawa sun ce “Ba a fafe gora ranar Tafiya”.Bakin alkalami idan ya bushe ai shikenan.Nagartar abin sayarwar da aka kai kasuwa ita ce zata sa mutane suyi ta rubibin son sayen shi.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Wannan ya na nuna ke nan abu ya zo inji mai tsoron wanka.ita kasar Nijeriya maganar wani sashe ko bangare na kasa yace yana goyon bayan dan takarar daya fito daga sashen,ba wannan lokacin bane aka fara yin shi ba, wani dadadden al’amari ne.

Babu wani sashe na Nijeriya da zai bugi kirji har yace al’ummar bangaren shi ne, ko su kawai sun isa su share ma shi hawaye,har kuri’arsu ta kai shi ga samun nasarar zaben a lokacin.

Irin wannan tunanin sam ba zai yiyu ba,kamar dai mutum ya ce zai iya kirga digon ruwa lokacin da ake ruwan sama.
Ana da ‘yantakarar Shugaban kasa 18 a zaben Shugaban kasar da za ayi watan Fabrairu 2023, hudu daga sashen Kudu maso yamma abinda aka fi sani da kabilar Yarabawa, da suka hada da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu APC,Abiola Kolawale PRP,Omoyele Sowore AAC,Olufemi Adenuga BP,Adebayo Adewole SDP Sai kuma Farfesa Christopher I, AP,.Sashen kudu maso gabas da akwai shida da suka hada da Peter Obi LP,Osita Nnadi APP, Chukwudi Umeadi APGA,Deberechukwu Nwanyanwu ZLP,Dumebi Kachikwu ADC,sai kuma Mazi Okwudili na NRM.Daga sashen Arewa kuma akwai Alhaji Atiku Abubakar PDP, Rabi’u Musa Kwankwaso NNPP,Yabagi Sani ADP,Ado Ibrahim Abdulmalik YPP, Mamman Dantalle APD,sai Hamza Almustafa dantakarar jam’iyyar A A.

Kodai ba ace komai ba da ganin ‘yan takarar goma sha takwas da ake dasu, goma shabiyu daga sashen kudu suke, inda abin ya kasance sashen kudu maso gabas na da shida na Kudu maso yamma kuma na da shida.Kamar yadda abin yake sashen Arewa gaba daya nada shida ko dai ba ace komai ba, sashen Kudu ko nace al’ummar can,ko shugabannin siyasarsu suna da kwadayin mulki ya koma wancan sashen.

Sai dai idan aka yi ma shi al’amarin tunani mai zurfi daga cikinsu ana iya zabo ‘yantakara mutum hudu wato Alhaji Atiku Abubakar,Bola Ahmed Tinibu, Rabi’u Musa Kwankwaso,da kuma Peter Obi.Daga cikin wadannan watakila tun a zagaye na farko cikin ikon Allah ana iya samun wanda yayi nasara,ko kuma sai an tafi zagaye na biyu, koma dai minene daga cikin su wadannan ‘yan takarar da akwai wadanda suna iya kasancewa tamkar ‘yan rakiya ne.

Babu wanda ya san abin da yake cikin zuciyar su ‘yantakarar domin wasu ma na iya cewa, magoya bayansu,su jefa ma wani daga cikin su gogaggun ‘yantakarar.

Wannan siyasar da ake ciki ko zabe na gaba wanda ke zuwa ba kasafai bane ake samun ‘yantakara ba, daga sashen Kudu da suka kai har goma sha biyu ba,duk da yake dai na yi magana kan abinda ya sa al’amarin ya kasance haka.

Kowanne bangare yana dogara ne da wani bangare na dan’uwansa domin ya inganta, haka ne al’amarin yake tafiya, shi ne yana samun taimako,manufa anan ita ce babu sashen da za ace shi kadai zai iya kai bante,amma idan ya samu hadin kan wani sashen ko wasu sassan shi ke nan bai da wata matsala.

Haka shi al’amari yake yawan mutane su ne kasuwa ba maganar tarin runfuna ba, kamar yadda marigayi Alhaji Mamman Shata ya bayyana cikin wakarsa mai suna “Isiyaku ka dawo Lafiya, ashe mutane sune kasuwa mu a raba mu da tarin runfuna,”har ma yana karawa da Ye yeyeye yeyyere, ye dan turmi sha daka, ye dutse sai mirgina”. Maganar gaskiya kuma haka ne shi al’amarin yake domin an gina kasuwa mai yawan runfuna ya kuma kasance babu mutane, ai tamkar an gudu ba a tsira ba ke nan.

Kamar idan aka dubi shi yankin ko sashen Kudancin Nijeriya akwai marigayi Dakta Nmandi Azikwe,Janar Aguiyi Ironsi Janar ritaya Aremu Olusegun Obasanjo, Earnest Shonekan, Goodluck Ebele Jonathan.Yayin da shi kuma sashen Arewacin Nijeriya akwai marigayi Sir AbubakarTafawa Balewa,ritaya Janar Yakubu Gowon,marigayi Murtala Ramat Muhammed,ritaya,marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, ritaya Janar Muhammadu Buhari, ritaya Ibrahim Badamasi Babangida,ritaya Janar Abdulsalam Abubakar,marigayi Janar Sani Abacha,da kuma marigayi Umar Musa ‘Yar’adua.

Koma ba a ce komai ba shi sashen Arewa yafi yawan wadanda suka Shugabanci ita kasar Nijeriya inda yake da tara,sashen Kudu yana da biyar,ko ba a ce komai ba sai an fadawa mutum wadanda suka fito daga sashen ne suka dade suna Shugabanci.

Shi kuma sashen Kudanci biyar ne da aka yi mata fifiko da hudu, amma idan ana maganar cigaba tsakanin da ita Arewa “Koda girgiza Hausawa sun ce Kanya tafi Magarya ‘ya’ya”wannan magana haka take babu ja tunda Kare ya mutu a saura (wurin da aka dan dade ba a noma shi).

‘Yan siyasa na kowanne sashe sune suka fi sanin hanyoyin da za su bi na bullo ma shi al’amarin yadda hakan zai kai su ga samun nasara,sai dai wani abu kada a saki reshe a kama ganye.Masu zabe sune yakamata ‘yantakara su rika zawarcinsu.

Wani abu da yake da daukar hankali shi ne yadda ‘yan kabilar Ibo na sashen Kudu maso gabashin Nijeriya,da basu damu da maganar yin zabe ba, amma sai ya kasance wannan lokacin suna yin gaba- gaba wajen maganar rajistar yin zabe.Bugu da kari yanzu akwai majami’un da basu barin wani ya shiga sai ya nuna shedar katin zaben shi. kafin a kai ga barin shi ya shiga.

Ita ma kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere ta sauya kudurin data fara furtawa na goyon bayan dantakarar LP Peter Obi, tace saboda gaskiya da dalci kamata yayi dan kabilar Ibo shi zasu goya ma baya.Yanzu abin ya dawo ‘yar-gida saboda kuwa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC suke goyan baya.

Shi kuma sashen na Arewa Shugabannin Dattawan Arewasu suka gana da ‘yan takara da suke ‘yan gaba- gaba na jam’iyyun APC, PDP, NNPP, da kuma LP,sai dai basu yanke shawara ba kan wanene suka ya dace a zabe.

Koma za suyi hakan watakila sai nan gaba, to Budurwa dai tamkar wata haja ce kowanne kuma da tayin da yake mata amma mai sayen ta daya ne.Nijeriya Allura ce cikin ruwa mai rabo shi ka dauka, a kuma tuna Allah shi ne ke bada mulki ga wanda ya so.

Siyasar kabilanci
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasar kabilanci
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Gwamnatin Kano Ta Dauki Karin Masu Share Tituna Don Tsaftace Muhalli

Ganduje Ya Ware Naira Miliyan 300 A Matsayin Kudin Karatun Daliban Kano Da Ke Karatu A Waje

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.