Mambobin Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), a Jihar Bauchi, sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Talata domin shaida wa duniya cewa har zuwa yanzu Gwamnatin tarayya ta kasa cimma bukatun da suke da su tare da neman yanayin koyarwa mai inganci.
Shiyyar ASUU na Bauchi ya kunshi jami’o’in Bauchi, Gombe, da jihar Filato sun yi zanga-zangar ne a Bauchi inda suka fito daga cikin jami’ar ATBU tare da fitowa kan titi na mintuna dauke da takardun da suke alamta bukatunsu daban-daban gami da yin wakokin neman goyon baya.
- Jaruman Nollywood Da Kannywood Sun Yi Wa Jos Tsinke Don Mara Wa Tinubu Baya
- Yawan Adadin Mutane A Fadin Duniya Ya Doshi Mutum Biliyan 8 — MDD
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida, Shugaban kungiyar ASUU a jami’ar ATBU, Dakta Ibrahim Ibrahim Inuwa ya roki masu ruwa da tsaki a Nijeriya da su matsa wa Gwamnatin tarayya lamba wajen ganin ta cika dukkkanin bukatun Malaman jami’o’i domin tabbatar da ci gaban kasa da inganta harkokin ilimi.
Ya ce, dole ne su yi tsawa su yi tsayin daka wajen kare tsarin jami’o’i a kasar nan ta hanyar bin matakan da doka suka shimfida.
Kazalika, ASUU din ta yi tir gami da fatali da kokarin gwamnati na sayar da jami’o’in kasar nan.
Dakta Ibrahim ya ce tun lokacin da suka janye yajin aikin watanni 8 sakamakon umarnin kotu da bukatar wasu ‘yan Nijeriya, Gwamnatin tarayya take sako-sako da batun biya musu bukatunsu a maimakon haka ma sai biyansu albashin watan Oktoba ta yi ba yadda ya dace ba.
Ya kara da cewa da gangan wasu ke nacewa wajen maida jami’o’i zuwa masu zaman kansu domin wasu daidaiku ne ke amfana da jami’o’i masu zaman kansu kuma hakan ba zai taimaka wa talakawa kasa wajen samun ilimi cikin sauki ba.
ASUU ta kara da nuna damuwarta kan cewa bisa fito da tsarin biyan albashi ta IPPIS wasu hakkokinsu da dama da doka ya ware musu an danne musu kuma ba za su lamunce da hakan ba.
Kungiyar dai ya ce tana da tulin bukatun da suke son Gwamnatin tarayya ta cimma musu amma har yanzu yanzu ba su ga sakamakon mai kyau ba. Don haka ne suka nemi masu ruwa da tsaki da fa su sanya baki domin ganin an shawo kan matsalolin.
Har-ila-yau, sun ce basu son sake shiga yajin aiki a Nan kusa domin cigaban amsa amma ba za su zura ido Kuma ana zalumtaersu ba, don haka ne a cewarsu suka dauki matakin yin zanga-zanga domin nuna wa duniya cewa har yanzu yanzu Gwamnatin tarayya ba ta shirya wa kawo karshen matsalolin da malaman jami’o’i ke fama da su ba.