Da yammacin yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a tsibirin Bali dake kasar Indonesia.
A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin tana raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Afirka ta Kudu bisa manyan tsare-tsare, kuma tana son su kara imani da juna a fannin siyasa, da sa kaimi ga samun ci gaba kan raya dangantakarsu a dukkan fannoni.
Ya ce Sin tana son yin mu’amala da kasar Afirka ta Kudu kan fasahohin tafiyar da harkokin siyasa da kasa, da goyon bayan Afirka ta Kudu wajen neman hanyar zamanintar da kanta bisa nata salo, da kara hadin gwiwa tsakanin shawarar “ziri daya da hanya daya” da shirin sake bunkasa tattalin arziki da farfadowa na kasar Afirka ta Kudu, da zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin cinikayya da zuba jari, da makamashi da sauransu, da sa kaimi ga aiwatar da ayyukan da aka cimma daidaito kansu a gun taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, wanda aka yi a kasar ta Afirka ta Kudu, da goyon bayan kamfanonin Sin don su zuba jari a kasar, da kuma fadada fitar da kayayyakin Afirka ta Kudu zuwa kasar Sin.
A nasa bangare, shugaba Ramaphosa ya bayyana cewa, Sin muhimmiyar abokiya ce ta kasar Afirka ta Kudu bisa manyan tsare-tsare, kuma kasarsa za ta ci gaba da goyon bayan ka’idar Sin daya tak a duniya. Kana Afirka ta Kudu tana son koyon fasahohin Sin a fannonin samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kyautata tsarin makamashi, da shiga ayyukan raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma kara bude kofa ga kamfanonin Sin don sa kaimi gare su, wajen zuba jari da hadin gwiwa a kasar.
Yau da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Senegal Macky Sall a tsibirin Bali dake kasar Indonesia.
Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, bisa kokarin bangarorin biyu, an samu babban ci gaba kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Senegal da kuma Afirka.
Ya ce Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da kasar Senegal wajen samun bunkasuwa da farfadowa, da goyon bayan juna kan batutuwan dake shafar cikakken ‘yancinsu, da tsaron kasa, da moriyar bunkasuwa. Ya kara da cewa, Sin tana son ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Senegal wajen gina ayyukan more rayuwa kamar hanyoyin mota, da yankin masana’antu, da kuma fadada fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasar Sin.
A nasa bangare, shugaba Sall ya godewa kasar Sin bisa gudummawarta ga Senegal da kuma sauran kasashen Afirka, yana mai cewa ta kasance kasa ta farko da ta goyi bayan shigar da kungiyar AU cikin kungiyar G20.
Ya ce kasar Senegal ta gamsu da ci gaban da aka samu kan ayyukan da aka cimma daidaito kansu, a gun taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, kana tana son ci gaba da hada gwiwa bisa tsarin dandalin tattaunawar.
A wannan rana kuma, shugaba Xi ya gana da firaministan kasar Netherland Mark Rutte, da firaministan kasar Australia Anthony Albanese, da shugaban kasar Argentina Alberto Fernández, da firaministan kasar Spaniya Pedro Sánchez, da kuma shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Seok-Youl. (Zainab)