• English
  • Business News
Friday, October 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sufeton ‘Yansanda Ya Ba Da Umarnin Tsaurara Tsaro A Hanyar Legas-Ibadan 

by Sadiq
3 years ago
'Yansanda

Sufeto-Janar na ‘yansanda, IGP Usman Baba, ya bayar da umarnin tsaurara matakan tsaro a kan titin Legas zuwa Ibadan mai cike da cunkoson jama’a, biyo bayan yawaitar sace-sacen jama’a da rashin tsaro titin.

Mai magana da yawansa, Olumuyiwa Adejobi, ya ce hakan ya biyo bayan bayanan da aka samu na tsaro a kan babbar hanyar daga kwamishinonin ‘yansanda masu kula da jihohin Legas, Ogun da Oyo.

  • Peng Liyuan Ta Halarci Taron Abokan Zama Na Shugabannin Kasashen G20
  • Sojoji Sun Kashe Shugabannin ‘Yan Bindiga Buzu, Ganai Da sauransu A Harin Jirgin Yaki

Ya ce babban sufeton ‘yansandan ya ba da umarnin sake fasalin jami’an tsaro cikin gaggawa a kan babbar hanyar domin samar da isassun jami’ai don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a kan hanyar tare da dakile sace-sacen mutane da sauran munanan abubuwan da ke faruwa.

Hakazalika, IGP din ya jaddada cewa, hukumar ‘yansanda ba ta damu da matsalolin tsaro da ake fama da su a hanyar Legas zuwa Ibadan ba, sai dai sun shagaltu wajen magance matsalar tsaro da dabarun kawar da barazanar da ke kan hanyar; don haka ne aka yi ta tantance hanyar.

Sufeton ya kuma yi alkawarin samar da isassun kayan gudanar da aiki ta hanyar fasahar kere-kere da kadarorin aiki ga kwamishinonin ‘yansanda masu kula da jihohin Legas, Ogun, da Oyo.

LABARAI MASU NASABA

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

Hakazalika, ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya masu kishin kasa, musamman masu amfani da hanyoyin, mafarauta, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da ke bin hanyar da su rika tona asirin barayin da suke addabar ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba a kan hanyar da kuma sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su.

‘Yansanda da sauran jami’an tsaro domin za su kama tare da kuma gurfanar da duk mai laifin da aka kama a hanyar a gaban kuliya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 
Manyan Labarai

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

October 30, 2025
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC
Manyan Labarai

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

October 30, 2025
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

October 30, 2025
Next Post
'Yansanda

Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Afirka Ta Kudu Da Na Kasar Senegal

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo

October 30, 2025
An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara

An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara

October 30, 2025
Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 

October 30, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara 

October 30, 2025
Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC

Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC

October 30, 2025
Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray

Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray

October 30, 2025
Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

October 30, 2025
Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

October 30, 2025
Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

October 30, 2025
Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

October 30, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.