Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce shirin sauya fasalin naira na iya durkusar da Dalar Amurka zuwa naira N200.00 kan kowacce dala daya.
Shugaban hukumar EFCC wanda ya bayyana hakan a wani shirin gidan rediyo na Sashen Hausa na Deutsche Welle (DW) ya ce darajar Naira za ta kara farfado wa sosai idan aka hada ta da Dalar Amurka.
Bawa ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amincewarsa ga babban bankin Nijeriya (CBN) na sake fasalin kudin.
A cewar sa, ba a sauya fasalin kudin ba acikin shekaru 20 da suka gabata duk da cewa doka ta amince da a dinga sauya fasalin kudin duk bayan shekaru takwas.
Shugaban na EFCC ya bukaci da a cire batun siyasa kan wannan kudiri na sauya fasalin kudin inda yayi kira ga ‘yan Nijeriya da su kai rahoton duk wadanda suka karkatar da kudaden gwamnati.
Ya bayar da kashi biyar cikin dari na duk wani kudin da aka kwato ga duk wanda ya ba da bayanai masu amfani don kwato irin wadannan kudaden da aka sace.