Bisa la’akari da irin muhimmiyar rawar da Nijeriya ke takawa a fagen samar da takardun tafiye-tafiye na zamani a duniya, an sake zaben kasar a matsayin mamba a Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Kasa da Kasa (ICAO-PKD) a karo na hudu.
ICAO-PKD, babbar cibiya ce ta adana da musanyar bayanan da ake bukata don tabbatar da ingancin Takardun Tafiya ta shafin intanet (e-MRTDs) kamar fasfo da sauransu.
- Tsadar ‘Yan Tsaki Da Abincinsu Na Neman Tilasta Dakatar Da Sana’ar
- Zamantakewar Aure Tsakanin Miji Da Mata: Wa Aka Fi Zalunta?
Zaben Nijeriya da sauran kasashe a hukumar, shi ne babban jigon taron hukumar ICAO-PKD karo na 29 wanda aka yi a birnin Speke Resort Munyoyo na Kasar Uganda, daga 16 zuwa 17 ga Nuwamba, 2022.
Hukumar mai zaman kanta ce da ke da alhakin gudanar da ayyuka ta ICAO don tabbatar da ingantaccen aiki na PKD, gami da gudanar da harkokin kudi da kwangila.
ICAO-PKD tana da kasashe 88 a matsayin mambobi, tare da mambobin kwamiti 15 wadanda ke yin wa’adin shekaru 3.
Mahalarta taron PKD ne ke zabar mambobin kwamitin kuma Majalisar ICAO ce ke nada su bisa tanadin dokarta.
A tsawon wadannan shekaru Nijeriya ta kasance mai taka rawar gani a tarurrukan hukumar ICAO-PKD kuma ta ba da gudummawa sosai, musamman kan batun tsarin sarrafa fasfo na yanar-gizo da kuma magance kan tsaron iyakoki.
Tawagar ta Nijeriya dai ta samu jagorancin babban Kwanturolan Hukumar Shige da Fice na Kasa, Isah Jere Idris.