Rashen babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG a nahiyar Afirka, da kwalejin nazarin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama ta jami’ar sadarwa ta kasar Sin, sun karbi bakuncin gudanar da taron tattaunawa, kan hadin gwiwar CMG da kafofin watsa labaru na kasashen Afirka na shekarar 2022 a birnin Nairobi na kasar Kenya.
Taken taron shi ne “Neman samun sabon ci gaba tare, da inganta karfin watsa labaru a duniya”, inda kafofin watsa labaru na kasashen Sin da Afirka, suka tattauna tare da musayar ra’ayoyi don sa kaimi ga samun sabon ci gaba kan hadin gwiwarsu.
A gun taron tattaunawar, a karo na farko, CMG da jami’ar sadarwa ta Sin, da jami’ar St. Augustine ta kasar Tanzania, da jami’ar Ibadan ta kasar Nijeriya, sun yi hadin gwiwa wajen gabatar da rahoton binciken ayyukan watsa labaru na CMG a nahiyar Afirka, tun daga shekarar 2021 zuwa ta 2022.
Rahoton ya yi nuni da cewa, a cikin shekara daya da ta gabata, CMG ya watsa labaru game da batutuwan Afirka, da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da ma duniya, don shaida cewa, ana mai da hankali ga bunksuwar Afirka, da hadin gwiwar dake tsakanin nahiyar da Sin, kana ana gabatar da ra’ayoyi game da manyan batutuwan duniya. (Zainab)