Jam’iyyar PDP mai adawa ta soki jam’iyyar APC bisa yunkurin dakile ‘yan kabilar Igbo mazauna jihar Legas daga karbar katunun su na zabe.
A cikin sanarwar da kakakin Jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fitar, ya sanar da cewa dan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu ya na tsoron goyon baya da jama’a ke nuna wa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ne.
Debo ya ci gaba da cewa, APC ta na son hana ‘yan Kudu Maso Gabas ne karbar katin zaben su ne, inda ya yi zargin cewa, APC na kokarin tayar da hargitsi domin ta yiwa zaben 2023 zagon kasa bayan APC ta san cewa, ‘yan Nijeriya, ba za su zabi Bola ba.
A cewarsa, magoya bayan APC a zabubbukan baya da aka gudanar a kasar nan, sun yi barazanar jefa ‘yan kabilar Igbo cikin Rafi in har ba su zabi APC ba, inda ya kara da cewa, an ci zarafin wasu ‘yan Nijeriya a yankin Isolo da ke jihar Legas a lokacin zabubbukan shekarar 2019, bayan sun nuna ra’ayinsu nakin Amincewa da APC.
Kakakin ya kuma gargadi tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu da kuma Jam’iyyar APC kan yin amfani da ‘yan bangar siyasa, inda ya kara da cewa, ‘yan Nijeriya, ba za su lamunci hakan ba.