Mataimakin shugaban jami’ar jihar Kwara (KWASU), Farfesa Muhammed Mustapha Akanbi (SAN), ya rasu.
Akanbi mai shekaru 51, ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata a wani asibiti da ke jihar Legas.
- ‘Yan Bindigar Da Suka Yi Garkuwa Da Malami Da Dansa A Kwara, Sun Bukaci Fansar Miliyan 100
- EFCC Ta Kama ‘Yan Damfara 18 A Jihar Kwara
Hukumar jami’ar ta tabbatar da mutuwar Akanbi a wata sanarwa da magatakardar jami’ar, Dokta Kikelomo Sally, ya sanyawa hannu.
Kafin a nada shi a matsayin mataimakin shugaban KWASU shekaru biyu da suka wuce, Akanbi malamin shari’a ne a Jami’ar Ilorin (UNILORIN).
“Cikin alhini muna mika wuya ga Allah, Hukumar Gudanarwar Jami’ar Jihar Kwara ta sanar da rasuwar Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammed Mustapha Akanbi (SAN).
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana rashin Akanbi a matsayin babban rashi mai raɗaɗi da kaduwa da mutuwar tasa.
“Mun mika wuya ga hukuncin Allah wanda yake bayarwa kuma yake karba. A kan wannan muke jimamin rasuwar mataimakin shugaban jami’ar da ya amsa kiran Allah a daren yau. Bawan Allah ne na gaskiya kuma mai kaskantar da kai, muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ba shi Aljannar Firdausi.
“Farfesa a fannin shari’a kwararre ne wanda ya taka rawa wajen bude wani sabon babi na daukaka KWASU. Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, kai tsaye zuwa ga KWASU da sauran malamai, da ’yan jihar Kwara da ma fadin kasar nan,” in ji gwamnan a wata sanarwa da babban mai yada labaransa ya sanya wa hannu, Rafiu Ajakaye.
A cikin sakon ta’aziyyar Sarkin Ilorin, Alh Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana alhininsa game da rasuwar Akanbi.
Sulu-Gambari ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro, abin bantsoro da damuwa, yana mai jaddada cewa mutuwar Akanbi babban rashi ne ga al’ummar Masarautar Ilorin, Kwara da kuma Jama’a baki daya.
Sakon ta’aziyyar Sarkin na dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Malam Abdulazeez Arowona, ya ce: “Shi (Akanbi) ya kasance kwafin mahaifinsa kuma tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC), Marigayi Mai shari’a Mustapha Akanbi.