Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da mataimakinsa, Ifeanyi Okowa, sun janye daga taron da aka shirya za a gudanar da ‘yan takarar shugaban kasa a bainar jama’a.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da gidan talabijin na kasa (NTA), ya wallafa a shafinsa na Twitter.
- Malaman Jami’ar Yobe Sun Yi Zanga-zanga Kan Rashin Biyansu AlbashiÂ
- Buhari Ya Halarci Wajen Kaddamar Da Hako Man Fetur A BauchiÂ
Kamfanin Yada Labarai na Daria Media da hadaka da News Central da kuma NTA ne suka shirya gudanar da ganawar wacce ake ci gaba da nuna wa kai tsaye.
Ba wannan ne karo na farko da Wazirin Adamawa, ya saba janye wa daga ganawar da ake yi da ‘yan takarar shugaban ba.
Ko a farkon wannan watan, Atiku ya umarci Okowa ya wakilce shi a wani taro na kai tsaye, a wani shirin da cibiyar bunkasa dimokuradiyya (CDD) ta shirya da hadakar gidan talabijin na ARISE.
Bugu da kari, a watan Oktoba, tsohon mataimakin shugaban kasar nan, bai halarci wani taro da gidan rediyo na Women Radio 91.7 ya shiya a Abuja don tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasa ba.