Matsalar karancin man fetur ta karade sassan birnin Legas da ke kudancin Nijeriya, yayin da al’umma ke nuna damuwa kan musabbabin karancin duk da cewa, ‘yan kasuwa masu zaman kansu na sayar da lita guda sama da Naira 210.
A halin yanzu, daidaikun gidajen mai ne ke sayar da fetur din a sassan Jihar ta Legas, yayin da dama ke ci gaba da kasancewa a rufe.
- Yadda ‘Yan Majalisa Suka Bai Wa Hammata Iska A Saliyo
- Shugabannin Sin Da Congo (Kinshasa) Sun Aike Wa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 50 Da Dora Huldar Kasashen Biyu Kan Hanyar Da Ta Dace
Rahotanni sun bayyana yadda motoci da babura suka yi dogayen layuka a kokarinsu na ganin sun sayi man.
Wasu daga cikin gidajen man na sayar da lita guda akan farashin Naira 210 ko 215 zuwa 220, sabanin farashin da gwamnati ta kayyade na Naira 169 zuwa 170.
A wasu jihohin na Arewa, musamman Kaduna, Kano, Jigawa da Katsina, gidajen man ‘yan kasuwa na sayar da man fetur din akan farashin 250 zuwa 260 akan kowace lita.