• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasashen Turai Sun Fusata Da Matakin Amurka

by CMG Hausa
3 years ago
An employee works in the X3 X4 assembly hall at the BMW Spartanburg plant in Greer, S.C. Wednesday, Oct. 19, 2022.  BMW's sprawling factory near Spartanburg, will get a $1 billion investment, and the German automaker will spend another $700 million to build a battery plant nearby as it begins the transition to electric vehicles in the U.S., the company announced.  (AP Photo/Sean Rayford)

A daren ranar 21 ga wata, a fadar shugaban kasar Faransa ta “Elysee”, shugaba Emmanuel Macron na kasar ya shirya wata liyafa, inda ‘yan kasuwar kasashen Turai da dama suka halarta, ciki hadda manyan jami’an kamfanonin Ericsson, da Volvo, da Unilever. Mr. Macron ya shirya liyafar ba domin murnar wani abu ba, sai don fatan wadannan kamfanoni ba za su bar kasashen Turai su je kasar Amurka ba.

Yanzu farashin makamashi ya karu matuka a kasashen Turai, wanda hakan ya sa kudin sarrafa hajoji ya karu sosai, lamarin da ya sanya kamfanonin kasashen Turai fuskantar matsananciyar matsala.

  • An Yi Ganawa Tsakanin Ministocin Tsaron Kasashen Sin Da Amurka 

Kamar yadda wani babban jami’in kawancen masana’antun sarrafa karfe na kasar Faransa ya fada, kila matsakaicin farashin iskar gas da wutar lantarki zai karu da ninki 4.

Amma a kasar Amurka, farashin makamashi bai sauya da yawa ba, kana kuma, shirin dokar yaki da hauhawar farashin kaya da gwamnatin kasar Amurka ta zartas, ya samar wa kamfanonin da ke Amurka kudin alawas da yawa, shi ya sa kamfanonin kasashen Turai ba abun da za su yi, sai dai janyewa daga nahiyar Turai, su koma kasar Amurka.

A watan Agustan bana, gwamnatin kasar Amurka ta gabatar da shirin dokar yaki da hauhawar farashin kaya, a kokarin samar wa kamfanonin kera motoci masu amfani da wutar lantarki a Amurka kudin alawas, amma shirin dokar bai shafi kamfanonin kasashen kungiyar EU, Japan, da Koriya ta Kudu ba. Irin wannan shirin doka maras adalci, ta sanya kamfanoni masu ruwa da tsaki juya hankalinsu daga masana’antun kera motoci masu amfani da wutar lantarki na Turai, zuwa kasar Amurka.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Kasashen Turai sun yi matukar fusata da hakan. Har ma shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zargi Amurka da laifin ba da kariya kan cinikayya.

Kana ministan tattalin arzikin kasar Jamus Robert Habeck ya ce, Amurka tana cin zalin Turai yanzu. Har ila yau jami’an EU sun zargi Amurka da laifin saba wa ka’idojin kungiyar cinikayyar duniya.

Kaza lika a ranar 22 ga wata, kasashen Faransa da Jamus, sun ba da sanarwar hadin gwiwa, inda suka nuna cewa, za a kiyaye masana’antun Turai da kauracewa shirin dokar Amurka ta yaki da hauhawar farashin kaya cikin hadin gwiwa. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani
Daga Birnin Sin

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Next Post
Zan Magance Rashin Aikin Yin Matasa Da Dala Biliyan 10 – Atiku

Zan Magance Rashin Aikin Yin Matasa Da Dala Biliyan 10 - Atiku

LABARAI MASU NASABA

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Kasashen Turai

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.