Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, na tsaka mai wuya na yiyuwar rasa damarsa ta komawa Majalisar sakamakon wanda ya lashe zaben fitar da gwani na Sanatan Yobe ta Arewa, Bashir Machina ya ki amince wa ya janye Lawan din.
Sanata Ahmad Lawan, shi ne ke wakiltar mazabar Yobe ta Arewa a Majalisar Dattawa a halin yanzu, ya tafi neman tikitin Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC inda Bola Tinubu ya kayar da shi da mummunar kaye shi da ragowar ‘yan takara.
Bayanai sun tabbatar da cewa tun bayan da aka kammala zaben fitar da gwani ake ta neman Lawan da ya lalubo tikitin Sanata domin samun damar sake shiga zaben 2023.
Sai dai kuma duk kokarin da Ahmad Lawan ya yi na lallabar Malam Machina ya janye masa tikitin tsayawa takarar Sanata hakan ya ci tura, domin ya ce ba zan janye ba.
A zaben fitar da gwanin Sanatan da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayu a garin Gashua, Machina ya samu nasara da kuri’u 289.
Wata majiya ta ce, mataimakin shugaban APC a shiyyar Arewa Maso Gabas, Mustapha Salihu, ya yi iyaka nasa kokarin don ganin ya karbo masa tikitin daga hannun Machina domin Lawan ya samu damar komawa majalisa.
A lokacin da aka tuntubi, Mustapha Salihu, kan wannan zargin, ya ce sam shi bai shiga harkokin jam’iyyar a matakin kasa ba.