Hukumar kare hakkin dan adam ta jihar Kano ta ce cikin watanni tara sun karbi bayanan aikata fyade har 721 daga sassan jihar.
BBC ta rawaito cewa, Shugaban hukumar ya shaida mata cewa cibiyar da ke lura da wadanda aka yi wa fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata mai suna WARAKA ce ta tantance tare da bin diddigin al’amarin.
- Matsalar Fyade Da Hanyoyin Magance Ta
- Dan Shekara 16 Ya Yi Wa Matar Yayansa Da Wasu ‘Yan Mata 9 Fyade A Ondo
Fyaɗe, matsala ce da ke ƙara ƙamari a Nijeriya musamman yadda ake cin zarafin mata da kananan yara ta hanyar fyaden.
Cibiyar WARAKA ta karbi korafin aikata fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata fiye da dari-bakwai, daga watan Janairu zuwa watan Satumbar shekarar nan.
Hukumar kare hakkin ɗan’adam ta jihar Kano tana aiki kafada-da-kafada da cibiyar ta WARAKA tsawon lokaci kasancewar ta mamba a kwamitin gudanarwar cibiyar.
Bugu-da-kari Malam Shehu ya ce kashi daya cikin uku na korafe-korafen suna gaban kotu, wasu kuma an yanke masu hukunci, amma ya ce akwai wani muhimmin aiki da cibiyar WARAKA ke tallafa wa mutanen.
Matsalar fyade ta jima tana ciwa al’umma tuwo a kwarya musamman a Nijeriya, inda fyade bai tsaya a kan manya ba ko ‘yan mata, galibi a wannan zamanin an fi cin zarafin kananan yara da jarirai.
Wasu dai na ganin rashin tsattsauran hukunci ga wadanda aka samu da laifin fyade ne yake sanya al’amarin ke kara ta’azzara.