Game da zargin da ministan tsaron kasar Amurka ya yiwa kasar Sin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya jaddada a gun taron manema labaru a yau cewa, kasar Amurka ta sha yada bayanan karya, don bata sunan kasar Sin ba tare da wata hujja ba, wannan ya shaida yunkurinta na tada rikici da manufar kama karya.
A jawabin da ministan tsaron kasar Amurka ya yi a taron tattaunawa na Shangri-La a kwanakin baya, ya nuna cewa, Sin ta nuna ra’ayin tilastawa da kai hari kan batun yankin tekun gabashi da kudancin kasar Sin, musamman mashigin tekun Taiwan.
Game da wannan batu, Wang Wenbin ya bayyana cewa, barazanar da ake fuskanta kan batun tsaron mashigin tekun Taiwan, ayyukan ‘yan aware ne da kuma goyon bayan kasar Amurka.
Kasar Amurka ta sabawa ka’idar “Sin daya tak a duniya”, da kasa cika alkawarinta, da sassauta takunkuman da aka yi a tsakaninta da yankin Taiwan, da kara sayarwa yankin Taiwan makamai, da taimakawa yankin Taiwan wajen neman goyon bayan kasa da kasa, da kuma nuna goyon baya ga yankin Taiwan don samun ‘yancin kai. (Zainab)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp