ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Samun Ci Gaba Na Bukatar Hangen Nesa

by CMG Hausa
4 years ago
Nesa

Shugaba Muhammad Buhari na Najeriya ya yi jawabi na musamman a jiya ranar Dimokuradiya, inda ya jaddada alkawarin tabbatar da tsaro a kasarsa. Kana a nasu bangare, jama’ar kasar sun ci gaba da nuna damuwa kan matsalolin rashin ayyukan yi, da tsadar rayuwa, a shafukan sada zumunta, inda suka bayyana koma bayan tattalin arziki a matsayin babban dalilin da ya haddasa rashin kwanciyar hankali a wasu wuraren kasar.

  • Japan Ba Ta Boye Yunkurinta Na Yin Fito-na-fito Da Kasar Sin Ba

Abin lura shi ne, ba Najeriya ce kadai ke fuskantar matsalar tattalin arziki ba. A halin yanzu, annobar COVID-19 da yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, sun jefa tattalin arzikin duniya cikin wani yanayi na rashin tabbas. Idan muka dubi alkaluman da aka samu a kwanakin nan, za mu ga jimillar GDP ta kasar Amurka ta ragu da kaso 1.4, sa’an nan yadda bankin tsakiya na kasar ya dauki matakai don daidaita matsalar hauhawar farashin kayayyaki, ya sa kasuwar hannayen jari ta kasar ta gamu da babbar matsala, inda farashin kusan dukkan hannayen jari ya ragu sosai. Yayin da a kasar Birtaniya, hauhawar farashin kayayyaki ta sa bankin Ingila ya daga jimillar ruwan da ake bayar kan kudin ajiya zuwa wani matsayin da ba a taba ganin irinsa ba cikin wasu shekaru 13 da suka wuce, tare da sanar da tabarbarewar tattalin arzikin kasar. A cikin wannan yanayi mai wuya da ya shafi dukkan kasashe, ya kamata a yi kokarin yin hangen nesa, da daukar nagartattun matakai, da hadin gwiwa da sauran kasashe yadda ake bukata.

Dole ne a magance matakai na son kai, da ma rashin hangen nesa. Misali, a Najeriya, wasu matasa sun dauki makamai sun zama ‘yan fashi sakamakon kwadayi. Amma idan ana da hangen nesa, za a iya ganin cewa ayyukan da suke yi sun haifar da barna ga jama’a, kana nan gaba tabbas za a yanke musu hukunci bisa muggun ayyukan da suka aikata. Ban da wannan kuma, misali a kasar Amurka, gwamnati ta bari cutar COVID-19 ta haddasa asarar rayukan mutane fiye da miliyan 1, da raunana tattalin arziki, tana neman raya tattalin arzikin kasar ta hanyar zuba makudan kudi cikin kasawanni kawai amma ba tare da daukar matakai na hana bazuwar annoba ba, abun da ya sa ake fama da matsalar hauhawar farashin kayayyaki mai tsanani a kasar. Sa’an nan, wasu kasashen yammacin duniya, yayin da suke fuskantar koma bayan tattalin arziki, suna neman ta da rikici tsakanin sauran kasashe, da raunana tattalin arzikinsu, don neman sanya karin jari komawa cikin kasuwannin gida. Amma a hakika, bayan an samu barkewar yaki a wani yanki, lamarin ya kan kawo cikas ga aikin samar da kayayyaki na duniya, da haifar da illa ga tattalin arzikin kasashe daban daban.

ADVERTISEMENT

Dalilin da ya sa kasar Sin ke iya samun ci gaban tattalin arzikinta cikin matukar sauri, cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, shi ne domin hangen nesa da ta yi, abin da ya sa take iya daukar nagartattun matakai masu dorewa, da daidaita moriyarta da ta sauran kasashe. Yayin da take hulda da kasashen Afirka, kasar Sin ta tsayawa kan manufar “tabbatar da daidaito, da moriyar dukkan bangarori”. Tana fatan ganin kasashen Afirka sun samu ci gaban tattalin arizki, kana tana goyon bayan hadin gwiwar da kasashen Afirka suke yi da sauran kasashe. Idan mun dauki bashin da kasar Sin ta ba kasashen Afirka a matsayin misali, za mu ga cewa, ko da yake kafofin watsa labaru na kasashen yamma su kan bayyana shi a matsayin “mulkin mallaka” da “tarkon bashi”, a hakika kasar Sin na ba da bashi ne bisa ainihin bukatun da kasashen Afirka suke da shi, da taimakawa kasashen Afirka inganta kayayyakin more rayuwa: Tun daga shekarar 2000, kamfanonin kasar Sin sun taimaki kasashen Afirka wajen gina ko kuma inganta layin dogo na fiye da kilomita dubu 10, da hanyoyin mota kimanin kilomita dubu 100, da gadaje kimanin dubu 1, da tashoshin jiragen ruwa 100, dai dai sauransu. Sa’an nan idan wata kasa ta gamu da matsalar biyan bashi, kasar Sin za ta tattauna da ita don samar da wata dabara mai dacewa don daidaita batun, har ma ta kan yafe wa kasa maras karfi bashin da take binta.

Hangen nesa ne ya sa kasar Sin take son zuba jari don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka, gami da ba da damar samun ci gaban harkoki ga kamfanonin kasar. (Bello Wang)

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Iran Da Su Aiwatar Da Cikakkiyar Takardar Bayanin Fahimtar Juna Da Aka Cimma

Sin Ta Yi Kira Da A Cike Gibin Cin Gajiyar Fasahar AI

Nesa
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Iran Da Su Aiwatar Da Cikakkiyar Takardar Bayanin Fahimtar Juna Da Aka Cimma
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Iran Da Su Aiwatar Da Cikakkiyar Takardar Bayanin Fahimtar Juna Da Aka Cimma

July 8, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Cike Gibin Cin Gajiyar Fasahar AI
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Da A Cike Gibin Cin Gajiyar Fasahar AI

July 8, 2026
Ministan Lafiya Na DRC Ya Gode Wa Sin Bisa Tura Kwararrun Likitoci Kasar Don Tallafa Wa Dakile Ebola
Daga Birnin Sin

Ministan Lafiya Na DRC Ya Gode Wa Sin Bisa Tura Kwararrun Likitoci Kasar Don Tallafa Wa Dakile Ebola

July 8, 2026
Next Post
Sin Ta Karyata Ikirari Da Canada Ta Yi Na Cewa Wai Wani Jirgin Sojin Sin Ya Tare Jirgin Sojinta

Sin Ta Karyata Ikirari Da Canada Ta Yi Na Cewa Wai Wani Jirgin Sojin Sin Ya Tare Jirgin Sojinta

LABARAI MASU NASABA

Auto Draft

DSS Ta Kama ‘Yar Jarida Zainab Sodiq Kan Zargin Mallakar Drone Ba Tare da Cikakkun Takardu ba

July 9, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa NSA Kan Shirin Samar Da Dakarun Tsaron Daji

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa NSA Kan Shirin Samar Da Dakarun Tsaron Daji

July 9, 2026
Shaidar EFCC Ya Ce Sirika Bai Sanya Hannu A Takardun Kwangilar Naira Biliyan 2 Ba

Shaidar EFCC Ya Ce Sirika Bai Sanya Hannu A Takardun Kwangilar Naira Biliyan 2 Ba

July 9, 2026
’Yan Bindiga Sun Kashe Farfesa Har Lahira A  Jihar Benuwai

’Yan Bindiga Sun Kashe Farfesa Har Lahira A Jihar Benuwai

July 9, 2026
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane A Kaduna Da Filato

Sojoji Sun Hallaka Shugaban ’Yan Bindiga, Sun Daƙile Hare-hare A Zamfara

July 9, 2026
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Iran Da Su Aiwatar Da Cikakkiyar Takardar Bayanin Fahimtar Juna Da Aka Cimma

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Iran Da Su Aiwatar Da Cikakkiyar Takardar Bayanin Fahimtar Juna Da Aka Cimma

July 8, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Cike Gibin Cin Gajiyar Fasahar AI

Sin Ta Yi Kira Da A Cike Gibin Cin Gajiyar Fasahar AI

July 8, 2026
Kotu Ta Tsare Malamin ABU Kan Zargin Gwamnatin Katsina Da Ɗaukar Nauyin Aikin Hajjin ‘Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Malamin ABU Kan Zargin Gwamnatin Katsina Da Ɗaukar Nauyin Aikin Hajjin ‘Yan Bindiga

July 8, 2026
Ministan Lafiya Na DRC Ya Gode Wa Sin Bisa Tura Kwararrun Likitoci Kasar Don Tallafa Wa Dakile Ebola

Ministan Lafiya Na DRC Ya Gode Wa Sin Bisa Tura Kwararrun Likitoci Kasar Don Tallafa Wa Dakile Ebola

July 8, 2026
Sin Ta Yi Watsi Da Ikirarin Philippine Kan Tekun Kudancinta

Sin Ta Yi Watsi Da Ikirarin Philippine Kan Tekun Kudancinta

July 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.