A cikin wannan mako ne ake sa ran shugaban Tarayyar Turai, Charles Micheal, zai ziyarci kasar Sin, bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi masa.
Wannan wani babban ci gaba ne a dangantakar dake tsakanin Sin da Turai, inda a karon farko, yawan cinikayya a tsakaninsu cikin shekarar da ta gabata, ya zarce dala biliyan 800, kana jari tsakanin bangarorin biyu, ya zarce dala biliyan 270.
Lallai wannan ya shaida yadda cinikayya da kyakkyawar dangantaka tsakanin bangarorin biyu ke kyautata da kara farfadowa tare da haifar da dimbin sakamako da ribar moriyar juna.
Sai dai a daidai wannan lokaci ne kuma, aka jiyo sabon Firaministan Birtaniya Rishi Sunak, ya na wasu furuci da suka sauka daga kan turba, inda yake bayyana kasar Sin a matsayin barazana ga martaba da kimar kasashen yamma. Idan har ikirarin da yake yi gaskiya ne, ta yaya aka samu karuwar wadancan alkaluma na cinikayya tsakanin bangarorin biyu?
Tun da ya hau karagar mulki, ya ke bayyana kasar Sin a matsayin kalubale. Shin manufofin kasashen waje al’ummar Birtaniya suka damu da shi, ko kuma kyautatuwar zaman takewarsu?
Firaministan na kaucewa ainihin alhakin da ya rataya a wuyansa na kula da al’umma da jagorantar kasarsa wajen samun ci gaba, inda yake mayar da hankali kan kasar Sin, wadda ba komai take nema ba, face zaman lafiya da hadin gwiwa da ci gaba na bai daya.
Ya kara da cewa, cinikayya tsakanin bangarorin biyu zai fuskanci sauye-sauye. An dai ga yadda Amurka ta tayar da rikicin cinikayya tsakaninta da Sin, kuma an ga gurguwar sakamakon da hakan ya haifar, inda ‘yan kasuwar kasar suka ji radadin a jikinsu.
Duniya na fuskantar tarin kalubale da suka hada da hauhawar farashin kayayyaki da masassarar tattalin arziki da yunwa da matsalar sauyin yanayi da makamashi, wadanda ba su bar kowacce kasa a baya ba. A wannan lokaci, kamata ya yi a hada hannu da ajiye bambance-bambance, wajen lalubo mafita tun kafin a rasa tudun dafawa.
Duk da wadannan kalubale dai, kasar Sin ta na kara daukar manufofin raya kanta da kyautata rayuwar al’ummarta, kuma cikin manufofin nata, har da kara fadada bude kofarta ga kasashen waje. Rufe kofa dai ko daukar ra’ayi na kashin kai ko kariyar cinikayya, sun riga sun shaida mana cewa, babu abun da suke haifarwa face koma baya. Kamata ya yi firaministan na Birtaniya, ya sake nazari ya waiwayi tarihi, ya kuma zame masa darasi.