Rundunar ‘yansanda Nijeriya ta gurfanar da Aminu Mohammed, wanda uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari ke zargin ya yi mata kalaman batanci a kafar sada zumunta.
Idan ba a manta ba, an ruwaito cewar jami’an tsaro ne suka dauki Adamu, dalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse, a Jihar Jigawa kan wasu kalaman batanci kan Aisha Buhari.
An bayyana cewar an gurfanar da Aminu ne a ranar Talata a gaban babbar kotun tarayya mai lamba 14 a Abuja.
A cewar kawunsa, Shehu Baba-Azare, rundunar ‘yan sandan ba ta sanar da ‘yan uwansa game da gurfanar da shi a gaban kotu ba.
Baba-Azare ya ce “A asirce aka gurfanar da shi a kotu, ba su sanar da mu ba, mun damu matuka da halin da yake ciki. Zai yi jarrabawar karshe a ranar 5 ga Disamba,” in ji Baba-Azare.
Tuni dai dubban mutane suka shiga tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari a kafafen sada zumunta.
Mutane da dama sun soki uwar gidan shugaban kasa, kan zargin yadda aka tauye wa dalibin hakkinsa.