Wani kwarto dan shekara 26 mai suna Mtandazo Sibindi dan a yankin Silobela ana zarginsa da kashe wani mai suna Trymore Sibanda dan shekara 27.
An ruwaito cewa, Trymore ya tunkari kwarton ne domin ya tambaye shi akan zargin lalata da yake yi da matarsa, inda shi kuma Mtandazo, ya sa bindiga ya harbe Trymore ya mutu har lahira.
- Gwamnatinmu Za Ta Kawar Da Talauci Da Zarar An Zabe Mu – Shettima
- An Tsinci Gawar Wata Mace Cikin Dakin Wani Otel A Sabon Garin Zariyan Jihar Kaduna
Rahotanni sun ce, lamarin ya auku ne a makon da ya gabata, inda ‘yansanda na kauyen Kwekwez suka kamo Mthandazo, bisa zarginsa da hallaka Trymore saboda ya nemi jin ba’asin dalilin da ya sa yake yin fasadi da matarsa.
‘Yansanda a kauyen a cikin sanarwar da suka wallafa a kafar sada zumunta ta tiwita sun ce, lamarin wanda ya auku a ranar 21/02/22 a kauyen Simana da ke a yankin Silobela.
Sanarwar ta ‘yansandan ta ce, tuni an gurfanar da Mtandazo a gaban kotun Majistare da ke da zamanta a kauyen Kwekwe, inda kuma kotun ta tura Mtandazo ajiya a gidan Yari har zuwa ranar 8 watan Disambar 2022 don a ci gaba da sauraron karar zargin da ake yiwa masa.