Hukumar kula da binciken sararin samaniyar kasar Sin (CMSA) ta bayyana cewa, da safiyar yau ne kumbun Shenzhou-15 na kasar Sin, ya yi nasarar hadewa da tashar binciken sararin samaniyar kasar kamar yadda aka tsara.
A cewar hukumar CMSA, kumbon wanda aka harba jiya da dare, ya sarrafa kansa cikin sauri, inda ya hade da gaban tashar binciken sararin samaniya ta Tianhe da misalin karfe 5 da mituna 42 na safiyar Larabar nan agogon birnin Beijing na kasar Sin. Kuma dukkan tsare-tsaren ya dauki kusan sa’o’i 6.5.
Hukumar ta kara da cewa, ‘yan sama jannatin dake cikin kumbon Shenzhou-15, sun shiga tashar Tianhe, kuma ‘yan sama jannatin dake cikin kumbon Shenzhou-14, sun tarbi ma’aikatan dake cikin kumbun Shenzhou-15. Wannan shi ne karo na farko da ‘yan sama jannatin kasar Sin dake cikin tashar binciken sararin samaniya, suka tarbi wani kumbo mai dauke da ‘yan sama jannati.
Da misalin karfe 11 da mituna 8 da daren ranar Talata, agogon birnin Beijing na kasar Sin ne, aka harba kumbon, ta hanyar amfani da rokar Long March-2F Y15, daga cibiyar harba kumbuna ta Jiuquan dake yankin arewa maso yammacin kasar. (Ibrahim)