Gwamnatin Jihar Kaduna, ta ce dakarun sojin Nijeriya sun gano gawarwaki biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kashe su.
Samuel Aruwan, kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta Jihar Kaduna, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya kuma tabbatar da cewa sojojin sun kwato wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su tare da lalata sansanonin ‘yan bindiga a dazuzzukan Chikun-Kachia-Kajuru.
- Hannu Daya Ba Ya Daukar Jinka
- Talauci Ne Ke Sa Wasu ‘Yan Nijeriya Yin Barace-Barace A Kasashen Waje —Shugaban NAHCON
A cewarsa, bayanan da rundunar ta samu ta nuna cewa sojojin sun yi artabu da ‘yan bindiga a kewayen Kwanti, karamar hukumar Chikun, inda ya kara da cewa ‘yan bindigar sun tsere zuwa cikin dajin, sun bar babura hudu da sojojin suka kwato.
Ya ce sojojin sun gano wasu maza biyu da aka yi garkuwa da su, Muntaka Abubakar da Nwabueze John, inda ya ce sun kuma gano tare da kwashe gawarwakin wasu mata biyu da ‘yan bindigar suka kashe.
Ya ce wadanda aka ceto sun sake haduwa da iyalansu, bayan an kai agajin farko ga daya daga cikinsu da ya samu raunuka.
Ya kara da cewa, wata tsohuwa mai suna Tabawa Laraba, mai shekaru 85, sojojin sun ceto ta a yankin Kuzo, inda aka duba ta tare da yi mata bayani kafin ta sake haduwa da iyalanta.
“Sojojin sun kara sintiri zuwa yankunan Abrom, Gabachuwa da kuma dajin Kujeni da suka hada da kananan hukumomin Kajuru, Chikun da Kachia,” in ji shi.
Ya ce a yayin da sojojin ke artabu da ‘yan bindigar da suka tsere zuwa cikin daji, inda suka kakkabe sansanoninsu, sannan suka kwato bindigu kirar AK-47 guda biyu tare da wayoyin hannu guda uku, kakin sojoji da kayayyakin hada bama-bamai.