Karamin ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Clem Agba, ya zargi gwamnonin jihohi da kara jefa ‘yan Nijeriya cikin kangin talauci.
Agba ya bayyana cewa shirin gwamnati na saka hannun jari na zamantakewa bai yi tasiri sosai ba saboda gazawar gwamnonin wajen yin aiki da Gwamnatin Tarayya.
- Gwamnatin Kano Ta Janye Dokar Hana Adaidaita Sahu Bin Manyan Titunan Jihar
- CCPIT: Cinikin Waje Na Samun Ci Gaba Yadda Ya Kamata A Kasar Sin
Da yake magana da manema labarai a Abuja a yau Laraba, Agba ya zargi gwamnonin da aiwatar da ayyukan bogi, maimakon inganta rayuwar jama’a a jihohinsu.
Ya ce, “Gwamnoni sun fi mayar da hankali wajen gina manya-manyan ayyuka kamar gadar sama, filayen jiragen sama da dai sauran su da ake gani a manyan biranen jihohi, maimakon gina hanyoyin da za su dakatar da asarar amfanin gona da manoma ke yi.”
Ya koka da yadda gwamnonin suka kasa cin gajiyar filaye da saka hannun jari a harkar noma.
Ministan ya bukaci ‘yan Nijeriya da su dorawa gwamnoni alhakin halin talauci da ke fuskanta a kasar nan.