Wata babban kotu da ke zamanta a Minna ta jihar Neja, ta bada umarnin kama Janar Faruk Yahaya, Shugaban Sojojin Nijeriya bisa kin bin umarnin kotu.
Mai Shari’a Halima Abdulmalik, da ta jagoranci karar, ta ce, umarnin ya biyo bayan sanarwar da ya zo gaban kotun ne bisa bin umarnin 42 ta doka ta 10 na farar hula ta jihar Neja na 2018.
Sannan kotun ta kuma baya umarnin cafke Olugbenga Olabanji, Kwamandan horaswa da ke Minna kan laifi iri guda.
Hukuncin kotun na cewa, “Wannan umarni ne cewa shugaban sojojin Nijeriya, Janar Farouk Yahaya da Kwamandan horaswa da koyarwa ta (TRADOC) Minna wadanda ake kara na 7 da na 8 da cewa za su kasance a gidan gyaran hali bisa kin mutuntata umarnin wannan kotu mai daraja da ta ba su a ranar 12/10/2022. Kuma za su cigaba da kasancewa a gidan gyaran halin har sai sun wanke kansu daga rashin mutuntaya umarnin kotu.”
Wannan umarni ya biyo bayan karar da ke tsakanin Adamu Makama da wasu 42 da kuma Gwamnan Jihar Neja hadi da wasu mutum bakwai.
Bukatar daure shugaban sojin a gidan yarin ya biyo bayan wata bukata da Lauya masu shigar da kara Mohammed Liman, ya gabatar a gaban kotun ne.
Liman ya yi rokon kotun ta tura Shugaban sojoji da Kwamandan horaswa zuwa gidan yari bisa kin bin umarnin da aka basu a watan Oktoba.
Wannan matakin dai na zuwa ne kasa da awanni 48 da babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ita ma ta umarci a daure Shugaban ‘yansandan Nijeriya Usman Baba a gidan yari na tsawon watanni 3 bisa kin bin umarnin kotu.