Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi fashi da makami ciki har da mace mai kai wa ‘yan bindiga makamai.
Sannan sun samu nasarar kubutar da wasu mutane 15 da aka yi garkuwa da su bayan shafe kwanaki 50 a hannun masu garkuwan.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yanke Wa Dan Takarar Gwamnan YPP Hukuncin Daurin Shekaru 42 A Akwa Ibom
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yanke Wa Dan Takarar Gwamnan YPP Hukuncin Daurin Shekaru 42 A Akwa Ibom
Kakakin Rundunar ‘Yansandan jihar, SP Muhammad Shehu, ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a shelkwatar rundunar da ke Gusau a ranar Alhamis.
A cewarsa, an kama wasu mutane shida da ake zargi da laifin hada baki, da kuma tsoratarwa da karbar kudaden fansa a garuruwan yankin karamar hukumar Anka.
Wadanda ake zargin sun hada da, Jamilu Muhammad na kauyen Gadar Manya, Zayyanu Barmo na kauyen Manya Babba, Abubakar Usman na kauyen Mandau, Lauwali Girkau na kauyen Girkau, Sala Girkau na kauyen Girkau da Abubakar Yahaya na kauyen Tungar Mani.
“Mutane shidan da ake zargin ‘yan fashi ne da ke sanya haraji a kan al’ummar da suke a garuruwan da yin garkuwa da su, inda suka tara miliyoyin Naira ta hanyar asusun banki da suka kirkira don haka.
“Bayan an yi musu tambayoyi, duk wadanda ake zargin sun amsa laifinsu sannan suka bayyana cewa suna aika wa da sakon barazana ga kauyukan ko dai su biya kudi ko kuma a kai musu hari sannan kuma sun amsa cewa sun karbi miliyoyin Naira daga wasu al’ummomi biyar.
“Ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi da nufin kamo sauran wadanda ake zargi da hannu a wannan aika-aika,” in ji kakakin rundunar ‘yansandan.
Kazalika, rundunar ta kuma kama wata mata mai matsakaicin shekaru mai suna Gaje Abdullahi, ‘yar kauyen Madaci da ke Jihar Katsina bisa laifin safarar makamai da alburusai zuwa ga wani shahararren dan bindiga da ake kira Dawa wanda ya addabi jihohin Zamfara da Katsina.
Sai dai matar a wata hira da manema labarai ta amsa laifin ta, inda ta ce Dawa ne ya tilasta mata aikata wannan aika-aika saboda tsoron kada su afka mata kamar yadda suka yi wa mijinta suka kashe shi tare da jimata rauni a fuska.
Gaje ta bayyana cewa, shi Dawa aikenta ya yi ta amso masa gyada kuma har ya yi mata alkawarin zai ba ta tiya goma dan yin Kulikuli kuma ya bata naira dubu goma kudin Mota, “Ashe harsashin ne ya aikeni amso ba gyada ba ce.”
Har-ila-yau, ‘Yansanda sun ceto mutanan dajin sabon garin Dustin Kaura da ke gundumar Danjibga a karamar hukumar Tsafe wanda ya kai ga ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.