Matar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta nuna damuwarta kan yadda al’umma suka mata rubdugu da da tofin Allah wadai gami da matsin lamba, har sai da ta janye karar da ta shigar kan Aminu Muhammad, dalibin ajin karshe a Jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa.
Wanda ya shigar da karar Fidelis Ogbobe, karar a ranar Juma’a, ya ce, matar shugaban kasa, uwa ce ga al’ummar kasa baki daya don haka ta dauki matakin janye karar bayan shiga cikin lamarin da al’ummar kasa suka yi.
- Shugabannin Kasashe Da Kungiyoyin Kasa Da Kasa Su Bayyana Jimamin Rasuwar Jiang Zemin
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 909 Kan Zargin Aikata Manyan Laifuka A Adamawa
Ya buga hujja da sashe na 108 da karamin sashe na 2(a) na dokar manyan laifuka wajen shigar da bukatar janye karar.
Da ya ke yanke hukunci kan lamarin, mai Shari’a Yusuf Halilu na babbar kotun tarayya, ya jinjina wa uwargidan shugaban kasan bisa janye karar gami da yafe wa wanda ake zargin.
Da ya ke bada umarnin sakin dalibin, alkalin kotun, ya bukaci iyaye da a kowane lokaci suke bibiyar takun ‘ya’yansu domin kare su daga kauce wa layi.
Shi dai Aminu Muhammad wanda aka rawaito cewa yana fama da rashin lafiya ya kuma sha duka bisa bayyana kalamai na rashin da’a ga matar shugaban kasa ciki har da cewa ta ci kudin talawa ta yi ‘bulbul’, wanda haka ne aka tuhume shi da bata mata suna a shafin Twitter.
‘Yansanda ne suka cafko Aminu a Jami’ar Dutse a ranar 18 ga watan Nuwamban 2022, bayan umarnin da matar shugaban kasa ta bayar.