Rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa, ta cafke mutum 909 bisa zargin aikata laifukan ta’addanci daban-daban a tsakanin watan Fabrairu zuwa Nuwamban a fadin jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Sikiru Akande, wanda ya gurfanar da wadanda ake zargin jiya a Yola, ya ce bindigogi kirar AK-47 guda 22, bindigogi kirar gida guda 48, adaidaita sawu da mashina 25, wasu karin bindigogi kirar gida 14, alburusai masu rai 326 ne aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan.
- Aisha Buhari: Matar Tsohon Shugaban Kasa Jonathan, Bata Tsare Masu Yi Mata Izgili Ba
- Masana’antun Kere-keren Fasahohin Zamani Na Sin Na Ci Gaba Da Bunkasa Cikin Sauri
Sauran abubuwan da kwamishinan ya gurfanar har da kokon kan mutane, Naira miliyan N4, 915 da wasu abubuwan da dama.
Rundunar ta kuma gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya su 845.
Wadanda ake zargin da yawancin laifukan da ake zarginsu sun kunshi fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan kai, fyade gami da keta haddin mata da sauran laifuka daban-daban ne suka kama a wurare daban-daban da ke jihar, sai dai kesa-kesan sata sune a kan gaba.
Kwamishinan wanda kuma ya gurfanar da wasu gungun sabbin wadanda ake zargi da laifuka 27, ya bada tabbacin dakile ayyukan ‘yan ta’addan musamman a lokuktan bikin Kirisimeti da na sabuwar shekara, ya ce, za a jibge wadatattun jami’an tsaron domin tabbatar da inganta tsaro da kiyaye rayuka da dukiyar al’umma.
“Daga watan Fabrairu, mutum 120 aka gurfanar kan zargin garkuwa da mutane, 71 kan fashi da makami, 38 kan fyade, da kuma mutum 538 kan sata,” a cewar kwamishinan.