Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tsige shugaban Hukumar Bayar da Lamuni Kan Harkar Noma, Aliyu Abdulhameed, kan zargin badakalar kudade.
An gano cewa tun ranar Alhamis, Buharin ya sallami Abdulhameed daga aiki.
- Yadda Ake Cin Gajiyar ‘Google Drive’ Wajen Amfani Da Kwanfuta
- Li Keqiang Ya Gana Da Shugaban Majalisar Kungiyar EUÂ
Ana zargin Abdulhameed da badakalar kudade tun lokacin da ya dare karagar mulki hukumar a 2015.
Bayanan da suke zuwa mana sun tabbatar da cewa tuni shugaba Buhari ya fara lalubo wanda zai maye kujerar shugaban NIRSAL.
“Hatta motocin iko da suke hannunsa duk an kwace. Ya bar ofis dinsa a cikin wata karamar mota kirar Ford kuma ya ji a ransa cewa zai sake dawowa kan kujerarsa nan ba da jimawa ba,” a cewar wata majiya.
Akwai zarge-zarge da dama da suka shafi kudade da ake yi wa hukumar a karkashin jagorancinsa.
Cikakken bayani na tafe…