Akwai alamun jam’iyyar PDP za ta iya zabar wani babban masanin harkokin shari’a, Barista Okey Muo Aroh (Ike Abatete), a matsayin wanda zai tsaya wa dan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, matsayin mataimaki a zaben 2023.
Wasu rahotanni na cewa daga cikin sunayen da aka aika cikin wandanda ake saran za su zama abokan takarar Atiku sun hada da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike; Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri da Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, da kuma gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, amma dai har yanzu ba’a kai ga cimma matsaya kan kowa ba.
- Zabar Mataimaki: Buhari Ya Gana Da Gwamnonin APC Kan Fitar Da Mataimakin Tinubu
- Atiku Zai Yi Wa Tinubu Kwab Ɗaya, Don Ba Tsaransa Ba Ne, In Ji PDP
To sai dai Aroh, ya kasance dan siyasa kuma shi ne wanda da shi aka kafa jam’iyyar PDP kuma ya taba zama mamba a majalisar zartarwa ta jihar Anambra da kuma ya rike mukamai a hukumomi da dama a gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Aroh, ya jima yana goyon bayan Atiku Abubakar tun a shekarar 1999, ya zama daya daga cikin wadanda suka jagoranci tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP guda biyu da suka gabata.
Aroh kwararren masanin siyasa ne wanda ya taka rawa wajen kafa jam’iyya da tafiyar da harkokin jam’iyyar NPP, NPN zuwa zamanin soji na UNCP, GDM, NCPCN, CNC zuwa zamanin jam’iyyu biyu na NRC da SDP.