Wata goggo mai shekaru 60 da wata mace mai juna-biyu na daga cikin wadanda aka kama a lokacin da ake gudanar da bincike inda jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa suka kwato kilogiram 5,527.15 na methamphetamine da tabar wiwi, da katan-katan na kwayar tramadol 132,090 da kwalaben kodin (codeine) 2,000 a fadin jihohi biyar da babban birnin tarayya, Abuja a cikin makon da ya gabata.
An kama goggon ne mai suna Misis Ibinosun Sandra Esther a garin Ibadan na jihar Oyo a wani samame da aka kai musu biyo bayan kama wani nau’in tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5.5 da aka shigo da su kasar daga Afirka ta Kudu.
Kayan da ta yi ikirarin cewa ‘yarta ce ta aiko mata da su wanda aka boye su cikin wasu manya-manyan kayan sauti guda biyu ta hanyar NAHCO da ke filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja Legas a cikin jirgin Airpeace Airline.
A wani labarin kuma, jami’an NDLEA a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba sun kama kilogiram 1.4 na methamphetamine da aka boye a cikin kayan abinci da kayan kwalliya da za a kai su kasar Brazil a jirgin Qatar Airways.