A yau litinin ne, jam’iyyar PDP ta yi Allah wadai akan ci gaba da barazanar da kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima a matsayin shugaban kasa ke yiwa kafafen yada labarai da ke kasar nan.
A cikin sanarwar da PDP ta fitar ‘yan Nijeriya na ci gaba da sa ido akan irin yadda kwamitin ke yiwa kafafen yada labaran barazana a yayin da suke kan gudanar da aikinsu.
Sanarwar ta ce, irin wannan kiyayyar da kwamitin ke nuna wa kafafen yada labaran bai dace ba, sashi na 22 na kundin mulkin Nijeriya, ya ba su damar gudanar da Aikinsu ba tare da wata tsangwama ba.
A cewar sanarwar, PDP na gayyatar ‘yan Nijeriya akan su yi dubi akan yadda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gaza halartar fagen tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasa, inda hakan ya fallasa asirin kwamitin wajen son tauyewa kafafen ‘yancinsu da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su na gudanar da ayyukansu.
Sanarwar ta yi kira ga kafafen yada labaran da su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da jin wani tsoro ba kamar yadda dokar kasa ta tanadar, musamman a yayin da zaben 2023 ke kara karato wa.