Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta sanar da shirin sauya wa cibiyoyin yin rajista guda 16 matsuguni a kananan hukumomi uku da ke fuskantar kalubalen tsaro a Jihar Yobe.
Alhaji Goni Usman, shugaban ayyuka na hukumar ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki a Damaturu, a ranar Talata.
- Ginin Hedkwatar Ecowas: Al’ummar Afrika Ba Za Su Taba Mantawa Da Tallafin Kasar Sin Ba
- Sauran Kwanaki 25 Cikin Wa’adin Kwana 31 Da Aka Ba Wa Jami’an Tsaro Na Kawo Karshen ‘Yan Ta’adda
Usman ya ce za a mayar da cibiyoyin hada-hadarsu a kananan hukumomin Geidam, Yunusari da Gujba zuwa wuraren da babu matsalar tsaro.
Sai dai ya ce hukumar za ta yi watsi da shirin yanayin da zai kawo nakaso ga tsaro a yankunan kafin zaben 2023.
Leadership Hausa ta ruwaito jami’in ya ce an mayar da kuri’u 1,109 zuwa rumfunan zabe, wanda ya kawo adadin rumfunan zabe a jihar zuwa 2,823.
A nasa jawabin, Shugaban Sashen Kimiyya da Fasaha, Alhaji Lamido Ibrahim, ya ce adadin tsofaffi da sabbin katin zabe guda 93,912 ne hukumar ta tattara daga shekarar 2019 zuwa 2022.
Ya ce an raba 49,399, yayin da adadin 44,513 ya rage.
Ibrahim ya yi kira ga wadanda suka cancanci kada kuri’a wadanda ba su karbi katin zabensu ba da su gaggauta yin hakan domin yin amfani da katin zabe.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Haruna Garba, ya sake yin kira ga jam’iyyun siyasa da su mika tsarin yakin neman zabensu ga ‘yansanda domin ba su kariya.
Ya ce ‘yansanda sun yi ta gano lungu da sako da masu tayar da kayar baya domin kawar da su kafin zabe.
Garba ya bukaci masu ruwa da tsaki da su wayar da kan mambobinsu kan bukatar bin doka da kuma gujewa tashin hankali kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.