Wata babbar kotu a Jihar Legas ta yi watsi da karar da wani dan haya mai suna Ademola Onitiju, ya shigar a kan mai gidan da ta ba shi haya sabo da ta ji sayar masa da gidan.
A shekarar 2021, Onitiju, wanda sojan sama ne (mai ritaya) kuma ma’aikacin shari’a, ya kai Theodosia Ogunnaike kotu a kan ta ki sayar masa da gida mai dakuna hudu a Dolphin Estate a Ikoyi, amma ta sayar wa da wani gidan bayan da shi dan hayar nata ta fara yin ciniki.
Dan hayar, mai shekaru 59, wanda ya fara zama a gidan a watan Disambar 2015, ya ce tun da fari, mai gidan ta yi masa tayin ya siya, amma kuma bai biya kudin ba bayan ya amsa cewa ya yarda zai saya.
Onitiju, ya ce da farko an nemi ya biya Naira miliyan 170 kudin gidan amma sai ya biya Naira miliyan 90 a maimakon haka, sai mai gidan ta ki amincewa.
Ya kara da cewa, a lokacin da ake tattaunawa, ya sayar da kadarori biyu na gadonsu domin ya samu damar sayan gidan a farashin Naira miliyan 135 wanda ya ce shi a haka zai saya.
Ya ce, ya nemi matar da bashi lambar asusun bankinta domin ya biya kudin ta nan, amma ba ta ba shi komai ba har sai da aka sayar da gidan ga wani Samuel Dare, wani Kanal din soja.
Ogunnaike, wadda bazawara ce ta ce gidan na ‘yarta ne amma ita ke kular mata da shi.
Matar, ta ce Onitiju ya kasance ya na biyan kudin hayarsa na Naira miliyan 4.5 a asusun ajiyarta na banki duk shekara kuma ba a kara kudin hayar ba a lokacin zamansa sabo da su na zaune lafiya.
Uwargidan ta ce an fara ba Onitiju tayin sayen gidan, amma ba shi da kudin da zai biya.
Daga nan sai ta dakatar da tayin da aka yi wa jami’in sojan sama mai ritaya bayan ya yi tayin kudi guda biyu na Naira miliyan 90 da kuma Naira miliyan 100, inda daga nan ne ta bude kofar sayar da gidan ga kowa.
A hukuncin da ta yanke Bola Okikiolu-Ighile, shugabar alkalan kotun, ta ce shaidun Onitiju da ke gaban kotu ba su da wani karfi da za su kare korafin da ya shigar ba kuma ba shi da gaskiya a shari’ar.
Daga baya kotun ta yi watsi da karar.