Dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdulsalam AbdulKareem wanda aka fi sani da AA Zaura ya ce babu wata barazana ko tsoratarwa da za ta sa ya janye daga takara ko hana shi jajircewa wajen yakin neman zaben shi.
Zaura, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume a gaban kotu da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ke yi masa, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano kan shirinsa na takarar kujerar Sanata a lokacin yakin neman zabe da kuma bayan zabe.
Ya ce bai ji ana yi masa wata barazana ko tsangwama ba a siyasa duk da cewa shi sabo ne a bangaren kuma yana kokarin wakiltar mazabar da tsofaffin gwamnoni biyu na jihar suka taba wakilta a majalisar Dattawa.
“Nima daga cikin masu karamin karfi na taso don haka na san kalubalen mutanen mu. Ba abin da zai iya tsayar da ni; Ba abin da zai tsorata ni in kasance tare da jama’ata, in taimakawa rayuwar jama’ata. Babu wata barazana, matsin lamba ba zai raba ni da talakawa ba wurin janye takara ta,” inji shi.