Allah Ubangiji tabaraka wata’ala ya bayyana kalaman Annabi Isah ga mahaifiyarsa yayin haihuwa: “fa nada ha man tahtiha alla tahzani kad ja’ala rabbuki tahtaki sariyya” Sai wanda ke karkashinta, ya kirata da cewa, karkiyi bakin ciki, lallai Ubangijinki ya sanya abinda ke kasanki ya zama farin ciki a gareki.
Wannan a bisa kira’ar wanda ya tafi cewa, Annabi Isah (AS) ya yi magana tun yana cikin tsumman jego sabida hujjar cewa, Ubangiji ya fada cikin Alkur’ani, ta bakin Annabi Isah tun yana tsummar jego da cewa, Ni bawan Allah ne, Ubangijina ya ba ni littafin dokokinsa kuma ya sanya ni na zama dan aikensa “Kala inni Abdullahi ataniyal kitaba waja’alani nabiyya”.
Malamai sun ruwaito wasu daga cikin bayin Allah da Annabawa da suka yi magana tun suna tsumman jego.
• Annabi Muhammadu (SAW): An ruwaito daga Sayyada Amina tana cewa, lokacin da na haife shi, ya sauko yana Sujjada irin ta tsoho wanda ya dade a cikin addini yana bautar Allah yana fadi cewa bayan ya daga hannunsa da idanuwansa sama, na shaida babu wani Ubangiji sai Allah kuma ni ma’aikin Allah ne, “Ash Hadu Alla’ilaha’illallah wa ash hadau anni Rasulallah”
• Bawan Allah Juraidu: Wani bawan Allah ne da wata mata ta yi masa sharrin zina, ta zo da dan jinjiri ta ce yaronsa ne, sai wannan bawan Allah ya umurci jinjirin da ya fada asalin mahaifinshi, take dan jariri ya bayyana cewa, mahaifinshi wani makiyayi ne a wuri kaza.
• Akwai yaron da ya yi wa Annabi Yusuf shaida yayin da Zulaikha ta yi masa kagen cewa shi ne ya neme ta “Wa shahida shahidun min ahliha…”
• Akwai wani sarki da ya rura wuta, ya ce duk wanda bai kafirta ba, to ya fada cikin wutar, akwai wata mata tana goye da dan jariri, ta zo fadawa sai ta tausaya wa jaririn ta tsaya, take jaririn yace Mama mu fada, mu ke da gaskiya, ba wuta ba ce Aljannah ce a gabanmu.
• Akwai dan jaririn da ya yi wa wata bakar fata shaidar cewa ba ta yi zina ba, an jefe ta da yin zina sai wannan Jaririn ya kubutar da ita.
• Akwai jaririn mashida, wata baiwar Allah ce da ta yi Imani da Annabi Musa, Fir’auna ya sa an yanka duka ‘ya’yanta a gabanta kan ta kafurta amma ta ki sai da aka zo kan dan jaririn sai tausayin shi ya kamata, sai dan jaririn ya ce Mama kina kan gaskiya kuma ki ci gaba da tsayawa kan gaskiya.
• Mubarakul Yamama: wani yaro ne dan garin Yamama a garin Musailamatul Kazzabi wanda ya yi karyar Annabta, Manzon Allah (SAW) ya tambayi dan jaririn ne don ya tabbatar wa da mutanen garin cewa shi Annabin Allah ne da gaske ba irin nagarinsu ba makaryaci.
• Annabi Sulaiman (AS): Allah ya fada cikin hukuncinsa cewa, ya fahimtar da shi tun yana dan shekarun yarinta “Fa fahhamnaha Sulaiman…” an ruwaito cewa, ya warware wasu hukunce-hukunce masu sarkakiya tun yana dan yaro. Yana daga ciki, akwai wata Shari’a tsakanin wata kyakkyawar Mata da Mijinta na aure, sai Matar ta kai kara gun wani Alkali sai ya ce zai ba ta gaskiya amma sai ya yi lalata da ita, sai Matar ta ki amincewa, ta tafi wurin wani alkali, shi ma ya ce mata irin abin da na farko ya nema a wurinta, shi ma ta ki amincewa, har sai da ta je wurin alkalai hudu dukkansu suna neman abin da na farkon ya nema daga wurinta amma duk tana kin amincewa, sai Alkalan hudu suka jefe ta da sharrin zina! Sai aka yanke mata hukuncin kisa ta hanyar jifa, an kamo ta za a jefe ta sai Annabi Sulaiman (AS) ya gani ya tambaya abin da ya faru. Take Annabi Sulaiman ya taro abokan sa yara ya shirya wasan kwaikwayo a gaban Babansa Sarki Dawuda, ya nuna duk irin abin da ya faru; ga wata an yanke mata hukuncin kisa za a jefe ta, ga shaidu Hudu, ga Sarki a kan kujera ga yaro a gefe ya ce, sarki hukuncin nan bai dace ta hakan ba; bayan an gama wasan kwaikwayo, Sarki Annabi Dawuda ya kira dan shi Annabi Sulaiman, ya ce Dana, in kai ne ya za ka yi? Sai ya ce, dukkan shaidun hudu a yi musu tambaya irin abin da suka gani kuma kowa ya amsa tambayar ba tare da dayansa ya ji amsarsa ba, sai dukka shaidun suka bayar da amsa mabanbanta. Sakon Annabi Sulaiman ya isa. Matar ta kubuta, an jefe alkalan dukkansu Hudun a Shari’ar Annabi Dawuda.
• Akwai kissar mata biyu da suka je daji suna wanke kayansu, kowacce tana da dan jariri, sai suka samu wani wuri suka kwantar da su, daga baya sai kura ta zo ta dauke dayan jaririn ta cinye, sai Matan suka fara takaddamma kowacce tana cewa, danta ne a raye.
Sai suka kawo kara wurin Annabi Dawud, Annabi Dawud ya yanke hukunci ya bai wa wacce ba ita ce uwar dan ba, jaririnta ne kura ta cinye. Sai Annabi Sulaiman ya ce, Baba in ni ne ba haka zan yanke hukuncin ba, sai Annabi Sulaiman ya ce a nemo mai takobi ya raba jaririn biyu kowacce ta dauki daya, sai wacce ba jaririnta ba ne ta ce ta yarda, asalin uwar jaririn kuma ta ce ta hakura ta bai wa dayar jaririn.
Annabi Sulaiman ya ce wacce ta yarda a kashe jaririn ba ta san zafinshi ba don haka ba danta ba ne, wacce ba ta yarda ba, ta san zafinshi don haka a mayar mata da danta, nata ne. Imam Dabrani, ya rawaito cewa, An baiwa Annabi Sulaiman alkalanta yana da shekaru 12 da haihuwa.
• Kissar Annabi Musa da Fir’auni yayin da ya cafke gemun sa tun yana dan karamin yaro, Fir’auna ya sa a kashe Annabi Musa sai Matarsa Asiya ta ce wannan yaro ne amma a jarraba shi da wuta da zinari.
• Annabi Ibrahim (AS), Allah yana cewa mun shiryar da shi tun yana dan yaro “wa lakad a taina Ibrahim rushdahu min kablu…” yayin da aka haifi Annabi Ibrahim (AS), Allah ya turo masa Mala’ika ya sanar dashi Ubangijinshi a zuciya sannan kuma ya koya masa Zikiri a harshe.
• Jarrabawar da Allah ya yi wa Annabi Ibrahim da yanka dansa, an ruwaito cewa, Annabi Isma’il bai wuce shekara Bakwai ba a lokacin saukar umarnin amma ya ce Baba ka aiwatar da abin da Ubangiji ya hore ka.
Akwai tarihai na Annabawa da na bayin Allah da yawa da Ubangiji ya ba su hikima tun suna tsummar jego wasu kuma tun suna kan shekarun Yarinta.
Wannan ya nuna cewa, Annabawa Allah ya halicce su ne da kyawon halaye amma a bangaren Bayinsa akwai wadanda ake tsururinsu akwai wadanda kuma haka aka haife su da wadannan kyawon halayen.
Kuma duk halayen da wani zai koya in aka hada su da na Annabawa, sai ka samu na Annabawa ya fi girma matuka. In mutum halwa yake da kokarin yi, sai ka ji Allah yana cewa, Annabi Musa ya yi azumin kwana 40 safe da rana; Annabi Zakariya’u ya yi azumin kwana 3 a jere amma Annabi (SAW) ya ce Annabawa suna yin irin hakan ne ba don halayensu su karu ba, sai don godiyar Ubangiji.
Annabi (SAW) don ya tabbatar wa al’ummarsa cewa, dabi’un Annabawa da su ake haifarsu ba koya suke ba, Dabi’ar dan Adam duk irin al’ummar da ya taso, irin halayyar wurin zai taso da ita, sai dai gaba in ya fada Duniya ya sauya, shi ya sa Allah ya ce, kowa a kan tafarkin Addini yake, sai daga baya iyayensa su sauya masa da wanda suke kai.