•Gangami A Legas Ya Fi Jawabi A ‘Chatham House’ – Atiku
•Atiku Ya Fusata Ya Fara Nuna Bacin Ransa A Fili – Tinubu
A ranar Litinin da ta gabata, cacar baki ta ci gaba kara zafafa a tsakanin manyan ‘yan takarar shugaban kasa a na jam’iyyar APC mai mulki da kuma babban jam’iyyar adawa ta PDP, inda suke ci gaba da jifar junansu da zafafan kalamai.
Manyan abubuwa guda biyu da suka wakana a ranar Litinin sun hada da gangamin PDP a Legas da kuma jawabin Tinubu a ‘Chathem House’ wanda su ne suka kara ruruta wutar cacar bakin tsakanin manyan ‘yan takarar guda biyu.
Dan takarar shugaban na APC, Asiwaju Bola Tinubu ya kalubalanci takwaransa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, inda ya furta cewa ya gaji kuma har ya fara nuna gajiyarsa a fili. Ya shawarci takwaran nasa ya jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda kafin ya sha kaye lokacin zabe.
Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin daraktan yada labaransa na yakin neman zabesa, Barr. Festus Keyamo SAN wanda ya mayar da martani ga kalamun Atiku na cewa bai gina Jihar Legas ba lokacin da yake gwamna.
Ya ce, “A wurin gangamin yakin neman zaben PDP a Jihar Legas, dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya rasa abun cewa ne wanda ya shirga wa mutanen Legas karya na cewa dan takarar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bai gina Jihar Legas ba ballantana har ya gina Nijeriya.”
Keyamo ya tunatar wa Atiku cewa duk da kulle-kullensu na rage kudaden Jihar Legas lokacin da yake matsayin mataimakin shugaban kasan Nijeriya, Tinubu ya samu nasarar bunkasa Jihar Legas a matsayinsa na gwamna.”
Ya ce kar mutanen Jihar Legas su bari Atiku yana kasarsu yana shirga musu karya, duk da yunkurin da ya yi na kokarin tarwaza Legas, amma Tinubu ya mayar da jihar cikin hanyacinta tare da samun zaman lafiya da kowa ke bukata.
“Bari na tuna wa Atiku cewa bayan da aka dauke Babbar Birnin Tarayya daga Legas lokacin juyin mulkin Orkar a 1990, gwamnatin tarayya ta bar samar da ababen more rayuwa a Legas domin samun damar bunkasa gina Abuja.
“Lokacin da Tinubu ya zama gwamnan jihar a shekarar 1999 ya fara ginawa tare da bunkasa Jihar Legas.
“Lokacin mulkin Tinubu ne aka samar da dubarar ci gaba da gudanar da aikin tekun Eko Atlantic, wanda aka ci gaba da yin aikin lokacin Fashola wanda ya gada daga wurin Tinubu.
“Sauran ayyukan Tinubu a Legas sun hada da gina babban hanyar Kudirat Abiola da hanyar Awolowo da ta Ikoyi da ta Akin Adesola da BI; Adeola Odeku da BI; Agege Motor da Ikotun-Igando da Yaba-Itire-Lawanson-Ojuelegba da LASU-IBA da Ajah-Badore da Oba Sekumade da Ikorodu da Bourdillon-Gerald da babban hanyar Lekki da kuma na Adetokunbo Ademola.
“Ya samar da hukumomi da suka hada da LAWMA, HIGHWAY MANAGERS, LASTMA, KAI, CBD, LAGBUS, LASEPA, LASAMBUS da dai sauransu duka an kaddamar da su ne domin bunkasa mabambantan bangarori. Wannan shi ne bincike da hujja.
“Shi dai Atiku da jam’iyyarsa ta PDP su ne suka kasa tsinana komi lokacin da suke rike da madafun iko. Muna shawartar Atiku ya san irin yakin neman zabensa, indan kuma ba haka ba zai fuskanci wulakanci a zabe,” in ji shi.
A martanin da kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa ya mayar, ya bayyana cewa gangamin yakin neman zabe a Jihar Legas ya fi jawabin da Tinubu ya yi a ‘Chatham House’ da ke Landan, domin ya abun kunya ya gabatar a can.
Kwamitin yakin neman zaben PDP ya kara da cewa Tinubu abun takaici ne ya yi jawabi a waje ya kamata ya zauna a gina ya yi jawabinsa, domin ya kasa sauke aikin da ya rataya a wuyansa har yana marmarin samun mulki a kasa mafi girma a Afirka.
Kakakin yakin neman zaben Atiku-Okowa, Kola Ologbondiyan shi ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin da ta gabata.
“Tinubu ya kunyata ‘yan Nijeriya da magoya bayansa a jawabinsa, inda ya kasa amsa tambaya kan hanyoyin magance matsalolin tattalin arziki da tsaro da sauran kalubale da kasar nan take fuskanta.
“Yakin neman zabenmu yana armashi, inda dan takararmu ya dace da mulkin Nijeriya, saboda ya iya sarrafa harshensa yadda ya kamata ba ya kunyata mu a idan duniya lokacin da aka tambaye shi zai iya bayar da amsa mai kyau.
“Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da duniya cewa bai da wata akala da tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya nuna rashin kwarewarsa da rashin iya shugabancin wanda ba zai iya gudanar da ayyukan da suka shafi kasa ba idan har ‘yan Nijeriya suka zabe shi.
“Ko kadan bai kamata ‘yan Nijeriya su zabi shugaban da ba zai iya sauke nauyin da ke wuyansa ba,” in ji shi.
Kakakin kamfen din PDP ya kara da cewa idan aka tambayi Atiku cikin basira yake amsa duk wata tamaya da aka yi masa, kuma a yanzu haka ya tsara yadda zai magance matsalolin da gwamnatin APC ta jefa ‘yan Nijeriya a ciki.
Sai dai kuma Tinubu ya bayyana dalilinsa na bukatar wasu mambobin jam’iyyar su amsa tambayoyin da aka yi masa kai-tsaye a ‘Chatham House’ da ke Landan ranar Litinin da ta gabata.
A crewar Tinubu, a cikin harkokin siyasarsa yakan wakilta wasu domin su amsa tambayoyin da aka yi masa, saboda irin nasa salon kenan na aiki da tawaga.
Bayan ya kammala jawabi ga ‘yan Nijeriya da baki a ‘Chatham House’, Tinubu ya bukaci Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi jawabi kan yadda zai magance rashin tsaro, sannan ya bukaci daraktan sadarwa na yakin neman zaben APC, Dele Alake ya amsa tambaya a kan yadda zai magance matsalar satar man fetur.
Haka kuma ya bukaci shugaban wakilan APC wanda tsahon kwamishinan kudi na Jihar Legas, Wale Edun ya amsa tambaya a kan yadda zai bunkasa tattalin arziki idan ya zama shugaban kasa.
Sauran wadanda suka amsa tambayoyin sun hada da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi da kuma shugabar mata na jam’iyyar APC, Dakta Betta Edu.